Yanzu-yanzu: ICPC ta kwace kadarar miliyoyin Naira daga gwamnan Bauchi

Yanzu-yanzu: ICPC ta kwace kadarar miliyoyin Naira daga gwamnan Bauchi

- Hukumar ICPC ta sanar da kwace wani gini mallakin Sanata Bala Muhammad wanda ya same shi a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja

- Kadarar da ta kwace shine ginin Zinaria International School da ke fuloti 298, yankin Wuye, Cadastral Zone B3 Abuja

- An dai zargi Sanata Mohammed da yin amfani da kujerarsa a matsayin minista wurin killace dukiyar gwamnati

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) a ranar Talata, 16 ga watan Yuni, ta sanar da kwace wani gini mallakin Sanata Bala Muhammad wanda ya same shi a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja.

Ginin ne Zinaria International School da ke fuloti 298, yankin Wuye, Cadastral Zone B3 Abuja.

Kamar yadda takardar ta bayyana a shafin hukumar ta Twitter, ta ce bincike ya nuna cewa Sanata Mohammed ya mika ginin makarantar ga hukumar a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya.

An zargi cewa makarantar mallakinsa ce da iyalansa duk da cewa filin mallakin ma'aikatar noma da kiwo ce.

Yanzu-yanzu: ICPC ta kwace kadarar miliyoyin Naira daga gwamnan Bauchi
Yanzu-yanzu: ICPC ta kwace kadarar miliyoyin Naira daga gwamnan Bauchi Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kamar yadda takardar ta bayyana, hukumar za ta bada shaidar kwace ginin kuma za su sameta ta hannun ma'aikatar aikin gona.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukuma a Adamawa

Bayan takardar shaidar kwacewa, hukumar za ta mika bukata gaban kotu don kwace ginin kamar yadda sashi na 48 na dokokin ICPC tare da gwamnatin tarayya ta fitar.

Tun farko, an zargi Sanata Mohammed da yin amfani da kujerarsa a matsayin minista wurin killace dukiyar gwamnati.

Idan za ku tuna a watannin baya ne dai aka zargin Sanata Bala da baiwa kamfanin da shi ne diraktanta kwangilan kudi sama da bilyan uku da rabi , kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ga masu rike da mukaman mulki.

Kwangilar ita ce sayan motoci 105 domin amfanin gwamnan da wasu jami'an gwamnatin jihar.

Kuma duk da hakan, ana cece-kucen cewa kamfanin bata wanzar da kwangilan kamar da aka bukata ba.

Jami'an da suka san lamarin kwangilan sun bayyana cewa kamfanin Adda Nigeria Limited, aka baiwa kwangilan kuma gwamnan jihar Bauchi na da hannun jarin kashi 20 cikin 100 a kamfanin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel