'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24

'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24

A kalla sojoji 24 ne suka rasa ransu yayin da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa rundunar soji hari a daura da Segou da ke tsakiyar kasar Mali, kamar yadda ma'aikatar tsaro ta sanar a ranar Talata.

"Mu na da tabbacin cewa 'yan ta'adda ne suka kai harin," a cewar ma'aikatar tsaron kasar Mali.

Sabon harin na zuwa ne a cikin kwanaki biyu kacal bayan wani mummunan hari da 'yan ta'addar suka kaiwa dakarun soji a ranar Lahadi.

An samu asarar rayuka a kowanne bangare tare da bacewar wasu sojoji uku yayin harin.

Sai dai, har yanzu ba a san dalilan 'yan ta'adda na kai hari kan tawagar sojojin ba a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Akwai kungiyoyin 'yan ta'adda da dama a kasar Mali da sauran kasashen da ke yankin Sahel. Yawancin 'yan ta'addar na da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta al-Qaeda.

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun fi karfi a yankin arewacin kasar Mali, amma yanzu hare - haren 'yan ta'adda ya fara tsananta a tsakiyar kasar.

Ana yi wa Mali kallon kasa mafi hatsari da rundunar sojojin majalisar dinkin duniya ke yaki da 'yan ta'adda da ta'addanci.

'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24
'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24
Asali: Facebook

Majalisar dinkin duniya ta fara kai rundunar sojojinta kasar Mali a cikin shekarar 2012 bayan yankin arewacin kasar ya fada hannun 'yan tawaye da kungiyoyin addinin Musulunci masu tsaurin ra'ayi.

A wani labarin na Legit.ng mai nasaba da wannan, dakarun Sojin kasar Nijar sun hallaka dumbin yan ta'adda a yankin Sabon Birni, wani gari da yan bindiga suka addaba a jihar Sokoto.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya bayar da umarnin janye shingen kan hanya da aka saka a kan iyakar Kano da Kaduna

Jaridar Humangle ta samu rahoto daga shaidar gani da ido a kan cewa Sojin Nijar ne suka kai farmaki a Burqusuma, wani kauye dake daura da Nijar a jihar Sokoto.

Sojojin na Nijar sun hallaka daruruwan yan bindigan ranar Litinin da misalin karfe 3:15 na dare, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Sun ce Sojin Nijar sun hallaka a kalla yan bindiga 100 kuma sun babbaka maboyarsu dake Burqusuma.

Sai dai, har yanzu hukumar Sojin kasar Nijar basu yi tsokaci kan harin ba amma Bashar Altine Isa, shugaban kungiyar MSJ da wasu mazauna garin sun tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel