Sojan da ya yi ritaya ya koka a kan rashin biyan wasu tsofaffin Jami’ai fansho

Sojan da ya yi ritaya ya koka a kan rashin biyan wasu tsofaffin Jami’ai fansho

Wani tsohon soja, Sapper Olusegun Soetan, ya koka da yadda aka gaza biyansa da sauran tsofaffin abokan aikinsa kudin fanshonsu shekara da shekaru bayan sun bautawa Najeriya.

Sapper Olusegun Soetan ya shaidawa jaridar Punch cewa kudinsa da sauran wasu sojoji daga yankin Kudu maso yamma da su ka yi yakin basasa tsakanin 1967 zuwa 1970, ya makale.

Mista Sapper Soetan wanda ya ce ya na cikin sahun farko da aka dauka aiki a gidan soja a shekarar 1963 ya yi ritaya a shekarun baya, amma har yau ba a biya shi hakkokinsa ba.

Wannan dattijo ya ce an yi masu ritaya ne ko kuma an sallame su daga aiki tsakanin 1978 zuwa shekarar 1992 kamar yadda dokar gidan soja ta No.4/1977 ta yi tanadi.

Tsohon sojan yakin ya ce duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da su ke ciki, kuma har ya bada umarni a biya su hakkokinsu, har yanzu ba a iya yin hakan ba.

Sojan da ya yi ritaya ya zargi shugaban hafsun sojoji na Najeriya, Janar Abayomi Olonisakin da kin cika wannan umarni. Ya ce an kawo wata doka da ta hana a ba su hakkinsu.

KU KARANTA: An sa miliyoyin kudi a kan wani kasurgumin 'Dan bindiga a Katsina

Sojan da ya yi ritaya ya koka a kan rashin biyan wasu tsofaffin Jami’ai fansho
Janar Abayomi Olonisakin
Asali: UGC

A cewarsa, a watan Mayun 2020, Janar Abayomi Olonisakin da shugaban harkokin fansho na gidan soja, Manjo Janar su ka sa hannu a wata sabuwar doka da ta hana a biya su kudinsu.

Ya ce wannan mataki da aka dauka ya sa “Wadanda aka yi wa sallama da wadanda su ka ajiye aiki domin ganin dama a yankin Kudu maso yamamcin kasar ba su morewa kamar yadda sauran tsofaffin jami’ai su ke cin kudinsu.”

“Mutanen Ibo da su ka balle daga gidan sojan Najeriya da ‘yan sanda, su ka yi fada da sunan Biyafara sun samu hakkokinsu, sai mu da mu ka yi wa Najeriya yaki ne aka kyale mu.”

Tsohon Soja ya fadawa Shugaba Buhari cewa shekaru 41 kenan da su ka bar aiki, babu mai kula da su: “Mun zama kamar kwarangal da ke jiran su fadi kasa.”

“An yi mana wulakanci da tsangwama a gida da dangi da gidan soja. Wasunmu sun mutu da hawan jini, wasu ba su tafiya, wasu sun daina gani, wasu sun kurmance bayan mun yi wa kasa bauta.”

Ya ce: “Mafi yawanmu mun haura shekara 70 yanzu kuma dukkanmu daga Kudu maso yamma mu ke.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel