Kwanan nan Obaseki zai dawo cikinmu, ba za mu bayar da tikiti kai tsaye ba – Shugaban PDP a Edo

Kwanan nan Obaseki zai dawo cikinmu, ba za mu bayar da tikiti kai tsaye ba – Shugaban PDP a Edo

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo, Mista Tony Aziegbemi, a ranar Litinin ya tabbatar da cewar Gwamna Godwin Obaseki da wasu manyan jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za su sauya sheka zuwa jam’iyyarsa.

Sai dai kuma Aziegbemi ya ce ba za a ba gwamnan tikitin takarar jam’iyyar kai tsaye ba yayinda sauran yan takara suka nuna ra’ayinsu kan wannan kujerar, jaridar Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar PDP ta sanya ranar 19 da 20 ga watan Yuni domin gudanar da zaben fidda dan takararta na gwamna.

Jam’iyyar APC ta hana Obaseki tsayawa takarar zaben fidda dan takarar gwamnanta wanda aka shirya yi a ranar 22 ga watan Yuni.

Kwanan nan Obaseki zai dawo cikinmu, ba za mu bayar da tikiti kai tsaye ba – Shugaban PDP a Edo
Kwanan nan Obaseki zai dawo cikinmu, ba za mu bayar da tikiti kai tsaye ba – Shugaban PDP a Edo Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Hakazalika, a wata hira da aka yi dashi a ranar Litinin ta wayar tarho, Aziegbemi ya ce ya zama dole Gwamna Obaseki ya bi tsare-tsaren da jam’iyyar ta shimfida idan ya sauya sheka.

Ya ce: “Babu wani tikiti kai tsaye da za a baiwa kowa; haka yake a kowani shiya na damokradiyya, kuma akwai wani tsari da kundin tsarin jam’iyyar ta shimfida kuma shine abun da muke bi.

“Amma zan iya tabbatar maku da cewa gwamnan, mataimakinsa, da gaba daya tsarin APC a jihar za su dawo PDP kwanan nan. Muna ta tattaunawa a yan kwanakin nan; amma zuwa gobe (yau), zan iya tabbatar da ainahin ranar dawowarsu tare da tawagarsa.”

A wani labarin kuma, a baya mun ji cewa wani sashe na jam'iyyar APC ta bukaci a kori Gwamna Godwin Obaseki da wasu mutum biyu na jam'iyyar sakamakon zargin su da ake da al'amuran zagon kasa ga jam'iyya.

KU KARANTA KUMA: Matsalar fyade 717 muka samu a cikin watanni 5 - IGP

Bangaren ya bukaci kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Oshiomhole da ya sallami Obaseki wanda cikin kwanakin nan aka haramtawa fitowa takara.

Sashin da ya samu jagorancin Kanal David Imuse ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa ba za su amince da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel