El-Rufa'i ya bayar da umarnin janye shingen da aka saka a kan iyakokin shiga jihar Kaduna

El-Rufa'i ya bayar da umarnin janye shingen da aka saka a kan iyakokin shiga jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta bayar da umarnin janye dukkan wani shinge da aka saka a kan iyakokin shiga jihar tare da bayar da umarnin maye gurbinsu da wasu sabbi domin cigaba da tabbatar da dokar hana bulaguro a tsakanin jihohi.

A cikin wani jawabi da Muyiwa Adekeye, mai taimakawa gwamna a bangaren yada labarai da sadarwa, ya fitar, gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da aikin dukkan kwamitin da aka kafa domin tsaron kan iyakokin jihar.

A cewar sanarwar, gwamnati ta dauki wannan mataki ne bisa shawarar da kwamitin yaki da annobar korona a jihar ya bayar.

Daga yanzu, shingen kan hanya da aka yarda dasu sune wadanda aka saka domin tabbatar da dokar takaita zirga - zirga a tsakanin karfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na safe, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gwamnatin ta kara da cewa ta samu rahotannin yadda jami'an tsaro da ke aiki a kan iyakoki suke tatsar kudi a hannun direbobi a wuraren da aka saka shingen hanya, lamarin da mahukunta a jihar Kaduna suka ce yana kara kawo dagulewar al'amura.

El-Rufa'i ya bayar da umarnin janye shingen da aka saka a kan iyakokin shiga jihar Kaduna
El-Rufa'i yayin rangadin iyakar jihar Kaduna
Asali: Facebook

A makon jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sassauta tsauraran dokokin da ya kafa don dakile annobar korona a fadin jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo

Kamar yadda gwamnan ya sanar ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2020, ya ce manyan shaguna za su iya komawa bakin sana'o'insu.

Masallatan Juma'a da Majami'u za su iya budewa a ranakun Juma'a da Lahadi kadai, amma karkashin kiyaye dokoki.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa, masu sana'ar aski da wuraren wanke kai duk za su iya budewa.

Otal za su iya budewa tare da wuraren cin abinci da kuma mashaya. Wuraren cin abincin za su iya budewa ne bayan an yi musu feshin kashe kwayoyin cuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng