Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo

Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu kuskure a cikin shawarar da uwar jam'iyyar APC ta yanke na korar takarar takwaransa, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Kazalika, Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar Edo da za a yi a watan Oktoba.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin gudanar da taron manema labarai a kan annobar cutar korona, wanda aka saba yi a fadar gwamnatin Kano.

"Jam'iyyar APC ba ta zartar da wani hukunci da ya sabawa kundin tsarin mulkinta ko na hukumar zabe ko kuma kundin tsarin mulkin kasa ba.

"Dole mu bi doka da tsari yayin gudanar da harkokin zabe. Babu wani batun saba ka'ida a kan maganar jihar Edo.

"Jihar Kano ta na yin iya bakin kokarinta domin ganin cewa jam'iyyar APC ta lashe zaben jihar Edo saboda an bi dukkan matakan da suka dace. Za mu lashe zaben," a cewar Ganduje.

Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo
Ganduje
Asali: Facebook

A ranar Juma'a ne APC ta sanar da cewa ta kori gwamna Obaseki daga cikin masu zawarcin neman takarar kujerar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar, saboda samun wasu matsaloli a takardunsa na karatu.

Kafin faruwar hakan, Obaseki ya bayyana shakkarsa a kan yiwuwar samun adalci a hannun uwar jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.

DUBA WANNAN: MC Tagwaye; mai barkwanci da kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)

Obaseki ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowarsa daga dakin da ya shafe sa'a biyu ana tantance shi a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Gwamna Obaseki ya bayyana cewa zai sanar da mataki na gaba da zai dauka dangane da batun sake neman takarar kujerar gwamnan jihar Edo bayan ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, gwamna Obaseki ya ziyarci wasu abokansa gwamnoni da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

A yayin da kwamitin zartarwa na uwar jam'iyyar APC ya aminta da salon zaben kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben dan takarar da yake so.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da hakan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

Baraka a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga zargin cewa bangaren shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na tsananta yakin neman kada Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel