Oshimhole da sauran shugabannin APC sun shiga ganawa da Gambari, sabon CoS na Buhari

Oshimhole da sauran shugabannin APC sun shiga ganawa da Gambari, sabon CoS na Buhari

A ranar Litinin ne shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya jagoranci wasu mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC (NWC) zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Ana kyautata zaton cewa taron, wanda ake yinsa a fadar shugaban kasa, Villa, da ke Abuja, zai tattauna rigingimun da jam'iyyar APC ta shiga sakamakon korar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, daga cikin 'yan takararta.

Daga cikin manyan jagororin jam'iyyar APC da suke tare da Oshiomhole a cikin dakin ganawar sun hada da mataimakin shugaba (shiyyar arewa maso yamma), Inuwa Abdulkadir; ma'ajin jam'iyya, Adamu Panda; da sauran wasu mutane biyu.

APC ta sanar da cewa ta kori gwamna Obaseki daga cikin masu zawarcin neman takarar kujerar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar.

A cewar APC, an kori takarar gwamna Obaseki ne saboda samun alamomin tambaya a tattare da takardunsa na karatu

A nasa bangaren, gwamna Obaseki ya bayyana cewa zai sanar da mataki na gaba da zai dauka dangane da batun sake neman takarar kujerar gwamnan jihar Edo bayan ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Oshimhole da sauran shugabannin APC sun shiga ganawa da Gambari, sabon CoS na Buhari
Oshimhole da Obaseki yayin wani zaman sulhu a baya
Asali: UGC

A 'yan kwanakin baya bayan nan, gwamna Obaseki ya ziyarci wasu abokansa gwamnoni da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

A yayin da kwamitin zartarwa na uwar jam'iyyar APC ya aminta da salon zaben kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben dan takarar da yake so.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da hakan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

DUBA WANNAN: MC Tagwaye; mai barkwanci da kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)

Baraka a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga zargin cewa bangaren shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na tsananta yakin neman kada Obaseki.

'Yan takara biyar ne ke adawa da Obaseki, wadanda suka hada da: Pius Odubu, Osagie Ize-Iyamu, Chris Ogiemwonyi, Matthew Iduoriyekemwen da Osabo Obazee.

Shugaban jam'iyyar APC na Edo ta tsakiya, Chief Francis Inegbeniki, wanda yake na hannun daman Adams Oshiomhole, ya tattara laifuka 50 na Obaseki wadanda sun isa su hana gwamnan zarcewa.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar ba su amince da Obaseki da mataimakinsa ba saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da shugaban jam'iyyar tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng