Minista Kwaku Agyeman Manu ya na dauke da kwayar ciwon COVID-19

Minista Kwaku Agyeman Manu ya na dauke da kwayar ciwon COVID-19

Ministan harkar kiwon lafiya na kasar Ghana, Kwaku Agyeman Manu, ya shiga cikin mutanen da su ka harbu da COVID-19. Kawo yanzu Ministan lafiyan ya na nan garau.

Rahotannin da mu ka samu daga jaridar Andalou Agency sun bayyana cewa gwamnatin Ghana ta tabbatar da samuwar kwayar cutar COVID-19 a jikin Kwaku Agyeman Manu.

A jiya ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2020 shugaban kasar Ghana, Mista Nana Akufo-Addo ya bayyana cewa ministansa Kwaku Agyeman Manu ya kamu da wannan cuta.

Akufo-Addo ya ce: “Bari mu yi wa ministan lafiyanmu mai kwazo, Kwaku Agyeman Manu, fatan ya samu lafiya, ya warke daga ciwon da ya kamu da shi a kan bakin aiki.”

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wa mutanen Ghana jawabi game da inda aka kwana a game da yaki da annobar COVID-19 a jiya.

Mai girma Akufo-Addo ya kuma bayyana cewa za a bude makarantun sakandare domin dalibai su cigaba da karatu kamar yadda su ka saba kafin wannan shigowar annobar.

KU KARANTA: An fadawa Gwamnati lokacin da ya dace a koma karatu

Minista Kwaku Agyeman Manu ya na dauke da kwayar ciwon COVID-19
Shugaban Ghana Akufo Addo
Asali: Facebook

Alkaluma sun bayyana cewa a kasar Ghana akwai mutane 11,964 da su ka kamu da cutar COVID-19. Wannan ya sa kasar ta zama cikin inda cutar ta yi kamari a nahiyar.

A daidai wannan lokaci kuma an yi wa mutane fiye da 250, 000 gwajin Coronavirus a kasar.

Abin farin cikin shi ne cutar ba ta kai ga buge Ministan lafiyan zuwa kasa ba. A Ghana, mutum 54 ne kadai su ka mutu a dalilin wannan mugun cuta mai kawo wahalar numfashi.

Mista Kwaku Agyeman Manu ya na kwance a wani asibiti inda ake kula da shi. Rahotannin da mu ke samu daga gidajen yada labaran kasar sun ce Likitoci su na jinyar ministan.

A Najeriya kuma mun ji cewa shugaba MuhammaduBuhari ya aikawa Sufetan ‘Yan Sanda sammaci dazu a fadar Shugaban kasa saboda yawan fyade a ‘yan kwanakin nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel