Kasar Benin za ta goyi bayan Ngozi Okonjo-Iweala a kujerar Kungiyar WTO
- Kasar Benin ta ce za ta marawa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ne a zaben WTO
- Benin ta ce ta yi na’am da shawarar AU na cewa a fito da ‘Dan takara guda
- Dr. Okonjo-Iweala ta na fuskantar barazana daga Abdel-Hamid Mamdouh
Takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a kungiyar kasuwanci ta Duniya watau WTO ta samu kwarin-giwa bayan da kasar Benin ta janye kanta daga zaben, ta kuma marawa zabin Najeriya baya.
Jaridar This Day ta ce kasar Benin ta bayyana matsayinta na fita daga takarar ne a wata wasika da Jakadanta a majalisar Dunkin Duniya da sauran hukumomin Duniya ya fitar a ranar Juma’a.
A wannan takarda mai shafi biyu, Benin ta sanar da cewa Eloi Laourou ba zai shiga neman kujerar WTO ba. Kasar ta cin ma wannan ne bayan shawarar da shugabannin yankin su ka yanke.
A wani taro da kasashen AU su ka yi a garin Addis Ababa, an ci ma yarjejeniyar cewa kasashen Afrika za su gabatar da ‘dan takara guda ne a zaben kungiyar WTO wanda za a ayi a bana.
KU KARANTA: Abin da ya sa na dawo daga rakiyar Buhari, na bi Atiku - Momodu
Wannan zama da aka yi ya sa Benin ta zabi ta marawa tsohuwar ministar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala baya. Ana tunanin shugaba Patrice Guillaume Athanase Talon ne ya taimaka da hakan.
Gwamnatin Benin ta kuma sanar da sauran ‘yanuwanta cewa za ta goyi bayan Okonjo-Iweala ne a zaben da za ayi domin maye gurbin Roberto Azevedo wanda zai sauka daga kujerar a Agusta.
A halin yanzu hukumar WTO ta yi na’am da shiga takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, wanda kafin yanzu ta rike mukamai da-dama a gwamnatin tarayyar Najeriya da ma babban bankin Duniya.
Kasar da ta nemi ta kawowa Najeriya cikas a wajen wannan takara ita ce Masar. Kasar Masar ta zargi Najeriya da kawo sunan Ngozi Okonjo-Iweala bayan lokacin fito da ‘yan takara ya kure.
Wadanda za su yi takara da Okonjo-Iweala a wannan zabe sun hada da shi Abdel-Hamid Mamdouh wanda ya fito daga Masar da Jesús Seade Kuri na kasar Mexico a Nahiyar Amurka.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng