COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna

COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bayan sassauta dokar kulle da yayi a jihar Kaduna, mataki na gaba shine kiyaye yaduwar annobar korona wacce take hannun mutanen jihar.

El-Rufai ya roki jama'ar jihar da su dauki dawainiyar yaki da yaduwar cutar korona. Ya ce kada a mayar da kokarin da yayi a baya ta hanyar kin kiyaye dokokin hana yaduwar cutar.

Gwamnan wanda ya mika wannan rokon a ranar Talata, ya mika sakon godiyarsa ga jama'ar jihar Kaduna a kan yadda suka yi hakurin watanni biyu da rabi wurin dakile annobar.

"Mu mutunta sadaukarwar da muka yi ta hanyar tallafawa kanmu tare da dakile yaduwar muguwar cutar. Kun yi babban kokari ta yadda kuka zauna a gida na makonni goma.

"Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassauta dokar da aka yi," ya kara da cewa.

El-Rufai ya yi kira ga dattawan da suka wuce shekaru 50 da su zauna a gida duk da sassauta dokar hana walwalar da aka yi a jihar Kaduna.

COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna
COVID-19: Yaki da korona na hannunku - El-Rufai ga jama'ar Kaduna Hoto: The Advocate
Asali: UGC

"A yayin da muka bude jihar, muna shawartar tsofaffi da su zauna gida tare da kiyaye zuwa gidajen mutuwa, jana'iza da kuma sallar jam'i."

"Idan ya zama dole ku hadu da wasu, ku saka takunkumin fuska tare da yin nesa-nesa da juna. Matasa da ka iya kamuwa amma basu dawata alamar cutar na iya yada cutar ga jama'ar da suka manyanta," yace.

Yayin kira ga jama'a da su kiyaye dokokin, ya ce, "matukar cutar ta ci gaba da yaduwa, za mu cire sassaucin tare da kara dawo da dokar."

KU KARANTA KUMA: Ke duniya: Yadda aka yi wa jaririya mai wata 3 fyade

Gwamnan ya ce za a iya kara bude kasuwanci amma matukar an samar da na'urar gwada dumin jiki, sinadarin tsaftace hannu da kuma kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

Ya kara da cewa, "Coci za su iya budewa ne a ranakun Lahadi kadai yayin da masallatai za su iya budewa a ranakun Juma'a kadai a halin yanzu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel