Borno: Jerin ayyukan da Farfesa Babagana Zulum ya yi a shekara guda - SSG

Borno: Jerin ayyukan da Farfesa Babagana Zulum ya yi a shekara guda - SSG

Mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya faro ayyuka 326 da kuma sababbin tsare-tsare da manufofi 49 a cikin shekara gudan farko da ya yi a jihar Borno.

Sakataren gwamnatin Borno, Usman Jidda Shuwa ya sanar da wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Asabar, ya na bayyana irin kokarin da gwamnatin Babagana Umara Zulum ta kawo.

Usman Jidda Shuwa ya ce daga cikin ayyukan da Babagana Zulum ya kawo akwai manyan kwangiloli 21 na more rayuwa, da gidaje 6, 544 da ake ginawa a kananan hukumomi 12.

Akwai ayyuka 76 da gwamnatin Borno ta dauka a harkar ilmi wanda su ka hada da gina sababbin makarantu 21 da kuma daukar nauyin 'dalibai 23, 776 masu rubuta jarrabawar SSCE a jihar.

A fannin lafiya, gwamnatin Borno ta na gina dakunan shan magani 37. Akwai tituna 30 da ake ginawa ko kuma yi wa faci a fadin jihar Borno, kuma ana shirin gina gadar sama ta farko.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya sassauta dokar zaman gida, ya ce a bude masallatai

A sha’anin tsaro kuwa gwamna Babagana Zulum ya rabawa jami’an tsaro motoci 300, sannan ya kara alawus din ‘yan sa-kai. Zulum ya kuma samar da matsuguni 4, 287 ga masu gudun hijira.

Gwamna Babagana Zulum bai yi watsi da harkar noma a Borno ba, SSG ya bayyana cewa an saye manyan motocin noma 56 da kayan noman rani da aikin noman shinkafa domin inganta noma.

Sauran ayyukan da gwamnati mai-ci ta kawo jihar Borno sun hada da kwangiloli 38 da aka bada na kawo karshen wahalar ruwa wanda su ka hada da gina manyan fanfon tuka-tuka fiye da 210.

Akwai ayyuka 18 a kan wutan lantarki da kuma wasu takwas a fannin noma da ayyuka bakwai domin koyawa mutane sana’a a kananan hukumomi, har da gina wasu cibiyoyin koyon aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel