Ke duniya: Yadda aka yi wa jaririya mai wata 3 fyade

Ke duniya: Yadda aka yi wa jaririya mai wata 3 fyade

An yi wa jaririya mai watanni uku fyade a kauyen Adogi da ke jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

A halin yanzu, jaririyar tana asibitin koyarwa na jami'ar Jos inda take samun taimako daga masana kiwon lafiya.

Maimuna Adam, mahaifiyar jaririyar ta sanar da Daily Trust a Jos cewa lamarin ya faru ne a daren ranar 27 ga watan Mayu, yayin da suke bacci amma kofarsu ke bude sakamakon zafin da ake yi a yankin.

"Lamarin ya faru a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2020, yayin da muke bacci. Na tashi na ga babu jaririyata a tare da ni.

"Da na duba wayata sai na ga babu ita amma na san a kusa na ajiyeta," mahaifiyar ta bayyana.

Ke duniya: Yadda aka yi wa jaririya mai wata 3 fyade
Ke duniya: Yadda aka yi wa jaririya mai wata 3 fyade Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Maimuna ta ce tuni ta san wani abu mara kyau ne ke shirin faruwa daga nan sai ta fasa ihu inda ta tada makwabta.

Ta ce daga maza har matan kauyen sun ci gaba da tururuwar shigowa gidanta tare da yawo a kauyen don neman jaririyar. Daga bisani aka tsinceta a wani kangon gini tana zubar jini.

"An ganta a wani kango an cire mata dan kamfai kuma jini na zuba ta gabanta. Daga nan sai muka garzaya asibiti," ta kara da cewa.

Ta yi kira ga jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki na jihar Nasarawa da su taimaka mata wurin bankado wanda yayi wannan mugun aikin don tabbatar da adalci.

Matar ta ce bayan kwana daya da aukuwar lamarin, sun kai wa 'yan sanda rahoto amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel ya ce, "Ba a sanar mana da aukuwar lamarin ba. Na kira 'yan sanda a kauyen Adogi amma sun ce basu san aukuwar lamarin ba amma za su bincika."

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Pauline Tallen, Ministar kula da harkokin mata ta Najeriya ta alakanta hauhawar fyade da dokar kulle da aka saka don dakile yaduwar annobar korona a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun halaka 'yan sanda biyu a Neja

Tallen ta sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2020 bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya inda ta kawo matsalar fyade gabansu.

Ta bayyana cewa za a dauki mataki wanda zai hada da na shari'a da kuma kafafen yada labarai don shawo kan matsalar fyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel