Edo 2020: APC ta bukaci korar Obaseki da wasu mutum biyu
Wani sashe na jam'iyyar APC ta bukaci a kori Gwamna Godwin Obaseki da wasu mutum biyu na jam'iyyar sakamakon zargin su da ake da al'amuran zagon kasa ga jam'iyya.
Bangaren ya bukaci kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Oshiomhole da ya sallami Obaseki wanda cikin kwanakin nan aka haramtawa fitowa takara.
Sashin da ya samu jagorancin Kanal David Imuse ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa ba za su amince da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar ba.
Bangaren ya ce: "Obaseki, Ojezua da wasu mutane sun garzaya kotu wanda hakan ya saba wa kundun tsarin mulki.
"Sun take dokokin jam'iyya tare da nakasa al'adar damokaradiyya.
"A kan hakan, kwamitin ayyuka na jihar Edo na Jam'iyyar APC ta bukaci korar mutane kamar haka: Godwin Obaseki, Anselm Ojezua da Dr. Aisosa Amadasun, sakamakon zarginsu da yin karantsaye ga jam'iyyar.
"Dole ne mu jaddada cewa bayan rasa kujerar gwamnan da muka yi a Bayelsa, ba za mu kuskure mu bar mai matsala a takardun makaranta ya karba tikitin kujerar gwamnan mu ba.
KU KARANTA KUMA: 'Ba Buhari aka kaiwa hari ba'; Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan harbe - harbe a Villa
"Muna mika godiyarmu ga mambobin jam'iyyar APC na jihar Edo a kan kokarinsu na dawo da sunan jam'iyyarmu, ballantana a yayin mulkin kama karya na Obaseki."
A wani labarin Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri ya ce jam'iyyar PDP za ta karbe gwamnati a zabe mai zuwa na gwamnonin jihar Edo.
Ya ce yadda ya bayyana a zabukan da suka gabata a cikin kwanakin nam tare da halin da jihar Edo ke ciki zai assasa aukuwar hakan.
Fintiri, wanda shine shugaban kwamitin PDP ya sanar da hakan ne a Benin yayin da jam'iyyar ke taro zaben wakilai don zaben fidda gwani da ke gabatowa.
Ya yi kira ga wakilan jam'iyyar da su dage wajen tsayawa kan ra'ayin jama'ar jihar.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa, kwamitin ya samu shugabancin Fintiri , gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri da Sanata Sam Ayanwu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng