Rigimar Hadiman Aisha Buhari ya nuna Buhari ya rasa iko da komai – Fani-Kayode

Rigimar Hadiman Aisha Buhari ya nuna Buhari ya rasa iko da komai – Fani-Kayode

Mista Femi Fani-Kayode ya yi kaca-kaca da shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin gazawarsa na shawo kan sabanin da ake samu da iyalinsa a fadar shugaban kasa.

Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rasa ikon gidansa, da mai dakinsa da iyalinsa da kuma gidansa, ya ce shugaban ya kuma gaza rike Najariya.

Gawurataccen ‘dan adawar ya fito kafafen yada labarai na zamani ya yi wannan magana ne bayan rahotanni sun karade gari cewa ana rigima tsakanin hadimin shugaban kasa da iyalinsa.

Har yanzu da ake ta wannan ce-ce-ku-ce, shugaban kasar bai iya fitowa ya yi wata magana ba.

“Harbe-harbe a fadar shugaban kasa saboda matsalar cikin gida? Matar shugaban kasa da hadimi su na fada?” Fani-Kayode ya tambaya: “Babu wanda zai iya shawo kan matsalar?”

Femi Fani-Kayode ya kara da cewa: “Shugaban kasa ya rasa iko a gidansa, matarsa, iyalinsa da ma’aikatansa da gidansa da kuma kasarsa?”

KU KARANTA:

“Wa ya yi wa Najeriya asiri. Wa ya yi mana wannan?”

‘Dan adawar ya kara da cewa: “Wa ya ke rike kasarmu? Shin wanene ke da iko? Ina mu ka dosa? Kasar mutane miliyan 200 ace iyaka abin da za mu iya kenan?

Ya ce: “Najeriya ta zama dawa ko gidan dabbobi kenan? An tsine mana ne? Mun rasa duk wata tarbiya da sanin ya kamata?”

Tsohon ministan kasar ya ce abin da ya faru tsakanin mai dakin Buhari da mukarrabinsa abin kunya ne a lokacin da shugaban kasa ya ke raye.

Ba wannan ba ne karon farko da Femi Fani-Kayode ya caccaki Gwamnatin APC mai ci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng