Shugaba Buhari ya yi wa Rotimi Amaechi ta’aziyyar rasuwar danuwansa

Shugaba Buhari ya yi wa Rotimi Amaechi ta’aziyyar rasuwar danuwansa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin wadanda su ka yi wa Ministan sufurin Najeriya watau Rotimi Amaechi, ta’aziyya na rasuwar wani danuwansa.

Muhammadu Buhari ya yi wa Rotimi Amaechi ta’aziyyar rashin yayansa Dede Amaechi wanda ya rasu kwanan nan.

Shugaban Najeriya ya fitar da jawabi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Mala, Garba Shehu. Shugaban kasar ya yi wa mamacin da iyalinsa addu’a a wannan lokaci da su ke jimami.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa minisan sufuri Rt. Hon. @ChibuikeAmaechi ta’aziyya a game da rashin yayansa, Dede Amaechi.”

Hadimin shugaban kasar ya fitar da wannan jawabi ne a shafinsa na twitter, a ranar Asabar 13 ga watan Yuni, 2020 da kimanin karfe 6:00 na yamma.

KU KARANTA: An bindige Basarake na biyu cikin wata daya a Jihar Katsina

“A wannan lokaci na makoki, tunaninmu da addu’o’inmu su na tare da dangin Amaechi da mutanen jihar Ribas”

Jawabin ya kara da cewa: “Shugaban kasa Buhari ya yi kira ga tsohon gwamnan na Ribas kuma tsohon sarkin yakin neman zabensa ya samu kwarin gwiwar jure wannan rashi da duba irin tarihin da ‘danuwansa na sa ya bari.”

Bayan ta’aziyyar da ta fito daga mai taimakawa shugaban Najeriya wajen harkokin yada labarai, sauran manyan ‘yan siyasa sun fito sun aika da na su sakon.

Gwamnatin jihar Ribas ta yi magana ta bakin kwamishinan yada labarai da sadarwa, Paulinus Nsirim, inda ta ce daukacin jihar Ribas ce ta yi wannan rashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel