Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona

Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona

An samu asarar rai tare da raunata mutane da dama yayin wani mummunan artabu tsakanin wasu fusatattun sojoji da kwamitin yaki da annobar korona a jihar Borno.

Fusatattun sojoji a cikin motocin yaki sun yi barazanar bude wuta matukar ba a bude hanya sun shiga garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ba.

Kwamitin yaki da annobar korona a jihar Borno ya rufe hanyar shiga birnin Maiduguri domin cigaba da tabbatar da dokar hana fita ko shiga cikin jihohi.

Arangama tsakanin sojojin da tawagar kwamitin yaki da korona a jihar Borno ta jawo asarar ran direban kwamitin tare da raunata wasu mutane da dama da suka hada da wata mace mai juna biyu.

Jaridar PremiumTimes ta rawaito cewa sojojin, a cikin motocin yaki guda uku, sun tilasta bude hanyar tare da barin motocin fasinjoji su shiga cikin jihar.

A yayin kokarin tilasta bude hanyar ne har motar tawagar mayar da martani cikin gaggawa ta jihar Borno ta ci karo da ta motar sojoji, lamarin da yasa ta hantsila cikin jeji.

Premium Times ta ce dukkan jami'an tsaron da ke cikin motar sun samu rauni yayin da likitoci a asibitin kwararru na jihar Borno suka tabbatar da mutuwar direban motar.

Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona
Sojoji
Asali: Twitter

"Sojojin sun ture babura masu kafa uku (Keke Napep), lamarin da ya yi sanadiyyar raunata wasu mata uku, mace mai juna biyu da wani jariri da ke cikin baburan," kamar yadda PremiumTimes ta rawaito.

Kaka Shehu Lawan, wani alkalin kotun tafi da gidanka da ke wurin da aka rufe hanya, ya ce ko kadan bai kamata jami'an tsaron gwamnati su ci zarafin jama'a haka ba.

A cewarsa, "mu na aikinmu na tabbatar da dokar gwamnatin tarayya lokacin da sojoji a cikin motocin yaki suka zo suka yi amfani da karfi da tashin hankali suka bude hanyar da aka rufe, lamarin da ya yi sanadin shigar dumbin baki zuwa cikin jihar Borno.

DUBA WANNAN: Ba fansho, ba garatuti: An kori Janar a rundunar soji saboda sukar shugaban kasa

"Ba iya hanyar kadai suka rufe ba, sun ci mutuncin mambobin kwamitinmu. Sun lakadawa mai daukan hotonmu dukan tsiya, sun kwace na'urarsa ta daukan hoto, sannan sun yi yunkurin dukan 'yan sandan da muke aiki tare dasu."

Kwamandan rundunar soji, birgediya janar Sunday Igbinomwanhia, ya bayar da hakuri a kan abinda sojojin da suka yi tare da daukan alkawarin cewa za a dauki mataki a kan sojojin da suka aikata hakan.

Igbinonwanhia ya bayyana hakan ne bayan mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, ya gayyace shi domin bayyanawa gwamnati dalilin da yasa sojojin suka aikata hakan.

Kadafur, wanda ya ziyarci wurin arangamar, ya yi Alla - wadai da halayyar da sojojin suka nuna.

Dakta Salisu Kwaya - Bura, kwamishinan lafiya na jihar Borno, ya tabbatar da cewa sun samu rahoton faruwar lamarin tare da mutuwar direban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel