Janye hadiman Aisha Buhari ya kawo rikici a fadar shugaban kasa
Rashin kwanciyar hankali ya cika fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan janye dukkan jami'an tsaron lafiyar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da aka yi.
Janye jami'an 'yan sandan da ke kula da ofishin uwargidan shugaban kasar ya biyo bayan rikicin da ya shiga tsakanin matar shugaban kasan da dan uwan Buhari, Sabiu Tunde Yusuf.
Rikicin ya fara ne tun bayan da uwargidan shugaban kasar ta bukaci Tunde da ya kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar korona na killace kai tsawon kwanki 14 bayan an yi tafiya.
Aisha Buhari ta tsinkayi gidan dan uwan shugaban kasar tare da yaranta inda sa'in'sar su ta kai ga shigar jami'an tsaronta wadanda suka harba bindiga har sau uku a iska.
A ranar Lahadi, jaridar Daily Trust ta gano cewa an samu harbe-harben wanda aka yi wa dan uwan shugaba Buhari mai suna Sabiu.
Sabiu wanda aka fi sani da Tunde ya dawo daga Legas amma bai killace kansa ba, lamarin da yasa uwargidan shugaban kasar ta kai masa ziyarar ba-zata har gida.
KU KARANTA: Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock
Wata majiya ta ce, "A ranar Alhamis mun ji uwargidan shugaban kasar tana umartarsa da ya killace kansa amma sai yace shugaban kasa ya ce masa ba sai yayi hakan ba.
"Takurawar da tayi yasa suka fara cacar baki wanda aka sanar da shugaban kasa. Shugaban kasar ya ce bai ga wani dalili da zai sa Tunde ya killace kansa ba.
"Ya ce Zahra da Halima sun bar fadar shugaban kasar don ziyartar sirikan Halima bayan an yi rasuwa amma da suka dawo basu killace kansu ba.
"Hakazalika sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya je Legas amma bai killace kansa ba. Don haka bai ga dalilin da zai sa Tunde ya killace kansa ba."
Sifeta Janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, wanda ya ziyarci fadar shugaban kasar a safiya Juma'a, ya bada uamrnin damke dukkan jami'an tsaron ofishin Aisha Buhari.
Sakamakon faruwar hakan, Hajiya Buhari ta matukar fusata inda ta yi kira ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya da ya gaggauta sako mata hadimanta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng