Kalli hotunan yadda ake koya wa mata tukin mota a Saudiyya
A yayin da ake sa ran Saudiyya zata fara bawa mata izinin tuka motoci daga ranar 24 ga watan Yuni, kamfanin man fetur na kasar mai suna Aramco ya fara bawa ma'aikatanta mata horo kan tukin motan.
Wannan dai yana daya daga cikin canje-canjen da Yarima Salman ya kawo a kasar duk da cewa wasu mahukunta a kasar musamman malamai basu gamsu da wasu ababen da ya ke aikatawa ba.
KU KARANTA: Zamu iya kare dukkan gyare-gyaren da muka yi a kasafin kudin 2018 - Majalisa ta fadawa Buhari
Mai daukan hotuna na kamfanin dillancin labarai na Reuters, Ahmed Jadallah ya ziyarci inda ake koyar da mata ma'aikata kamfanin Aramco 200 yadda ake tuki a sansanin koyon tuki na Dhahran.
Bayan koyar da tuki, matan kuma na koyan yadda ake duba gejin mai da canja taya da kuma sauran dokokin amfani da mota kamar amfani da madaurin kujerar mota.
Wannan damar fara tukin da za'a bawa matan wani abu ne mai muhimmanci a garesu musamman idan akayi la'akari da cewa akwai mata masu zuwa aiki kuma a baya basu iya fita sai sun nemi direba ko kuma wani na miji da zai tuka su.
Wasu daga cikin wadanda su kayi gwagwarmaya wajen ganin Saudiyya ta bawa mata izinin tukin mota sun fuskanci barazana sosai wasu daga cikinsu ma suna tsare inda ake tuhumarsu da yiwa kasashen waje aiki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng