Borno: Shagalin bidiri bayan sojoji sun fatattaki mayakan Boko Haram a Monguno

Borno: Shagalin bidiri bayan sojoji sun fatattaki mayakan Boko Haram a Monguno

Mazauna garin Monguno sun kasa boye farin cikinsu bayan dakarun sojin Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram da suka tada zaune tsaye a garin a ranar Asabar.

Kamar yadda majiya mai karfi ta tabbatar, mazauna garin sun fito tare da nuna godiyarsu ga dakarun bayan nasarar da aka samu.

"Kowa yana cikin farin ciki a fadin garin, dakarun sun nuna kwazonsu a yau. Hankalinmu ya kwanta a halin yanzu.

"A sa'o'i kadan da suka gabata, hankalinmu duk a tashe suke amma yanzu komai lafiya. Tituna suna cike da jama'a inda ake murnar samun nasarar dakarun soji," wani ma'aikacin kungiyar taimakon kai da kai ya bayyana.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da wannan ci gaban. Ta ce an yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram din ne da taimakon dakarun sojin sama.

Majiyar ta ce dakarun sun yi nasara amma a halin yanzu ana duba yawan barnar da aka yi musu.

"Kamar yadda nace, komai yanzu lafiya kalau don haka hankali ya kwanta. Sun yi kokari kamar yadda suka saba kuma an samu nasara. A halin yanzu ana duba mutum nawa aka kashe," majiyar tace.

Borno: Shagalin bidiri bayan sojoji sun fatattaki mayakan Boko Haram a Monguno
Borno: Shagalin bidiri bayan sojoji sun fatattaki mayakan Boko Haram a Monguno. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina

Da farko dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai hari kananan hukumomi biyu na jihar Borno.

An gano cewa 'yan ta'addan sun tsinkayi garin Monguno wurin karfe 11:30 inda suka dinga harbe-harbe babu kakkautawa.

Wani ma'aikacin INGO ya tabbatar da cewa karar bindiga ce ke tashi a garin ta ko ina.

"A yanzu haka da muke magana, 'yan Boko Haram sun kawo hari Monguno. Karar bindiga ce ke tashi amma dakarun soji na kokarin fatattakarsu. Muna bukatar addu'arku don babu lafiya," yace.

Hakazalika, mayakan ta'addancin sun kai hari wani kauye mai suna Usmanati Goni da ke karamar hukumar Nganzai a sa'o'in farko na ranar Asabar.

Kamar yadda wani mafarauci ya sanar, mayakan sun isa kauyen wurin karfe 10 na safe inda suka bude wa farar hula wuta.

A lokacin, ba za a iya tabbatar da yawan wadanda suka rasu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel