Aisha Buhari ta bukaci IGP da ya gaggauta sakin hadimanta da ya kama

Aisha Buhari ta bukaci IGP da ya gaggauta sakin hadimanta da ya kama

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya da ya gaggauta sako hadimanta da ya kama

- Ta sanar da hakan ne a wata wallafa da ta yi a shafinta na Twitter inda ta ce tana gudun su kamu da cutar korona yayin da suke garkame

- An gano cewa babban dogarin shugaba Buhari ne yasa aka damke su bayan sun yi yunkurin fitar da wani hadimi daga fadar bayan dawowa da yayi daga wata jiha

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, da ya gaggauta sako mata hadimanta.

Kamar yadda aka gano, babban dogarin shugaban kasa, Idris Kassim ne ya bada umarnin damke su tare da garkamewa.

Matar shugaban kasar ta sanar da hakan a jerin wallafar da ta dinga yi a shafinta na Twitter a ranar Juma'a.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, babban hadimin shugaban kasa, Yusuf Sabiu wanda aka fi sani da Tunde, wanda ya dawo daga wata jiha ya ki killace kansa amma sai ya kutsa cikin fadar shugaban kasar.

An gano cewa, hadiman Aisha Buhari sun saka karfi wurin fitar da Sabiu daga fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: APC ta kori Obaseki daga cikin 'yan takara kan wasu dalilai biyu

Amma sakamakon karfin ikonsa, ya sa babban dogarin shugaban kasar ya bada umarnin damke su.

Daga ciki kuwa har da ADC din uwargidan shugaban kasar, Usman Shugaba.

Kamar yadda uwargidan shugaban kasa ta wallafa, "Cutar korona ba karya bace kuma tana nan a kasar nan babu shakka.

"Ina kira ga dukkan cibiyoyin gwamnati da al'amarin ya shafa, da su tabbatar da an bi dokar killace kai bayan an yi tafiya daga wata jiha zuwa wata.

"Duk wanda ya yi tafiya ya zama dole a tirsasa shi ya killace kansa na kwanaki 14 ko waye kuwa. Babu wanda ya fi karfin doka kuma 'yan sanda ne yafi cancanta su tuna hakan.

"Daga karshe, ina kira ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya da ya gaggauta sakin hadimai na da ke hannunsa don gujewa kamuwarsu da cutar korona a wurinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel