Ku barni in huta, ba zan nemi kujerar Sanata ba - Masari ga Nagoya bayansa

Ku barni in huta, ba zan nemi kujerar Sanata ba - Masari ga Nagoya bayansa

Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce baya bukatar wani ofishin siyasa idan ya kammala mulkinsa a 2023.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa akwai rahotanni da ke nuna cewa Masari na hangen majalisar dattawa bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.

Masu kira ga Masari da ya nemi kujerar Sanata sun dogara ne da gogewarsa tun bayan da yayi kakakin majalisar wakilai da kuma wannan mulkin jihar Katsina da yayi.

Amma kuma, yayin jawabi ga manema labarai a ranar damokaradiyya ta 2020 a Katsina, gwamnan ya ce, baya bukatar amsa kiran kowa don neman kujerar Sanata.

Masari ya yi bayanin cewa zai cika shekaru 73 a yayin da zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu a matsayin gwamna.

"Bayan cikar wa'adin mulkina, zan zauna a gida in huta tare da bai wa matasa damar bada gudumawa a siyasa.

"Ban taba tsammanin zan shiga siyasa ba. Na fara aikin gwamnati amma daga baya aka nada ni kwamishina har sau biyu.

"Daga baya jama'a suka bukaci da in wakilcesu a majalisar wakilai wanda na yi nasara a zabe har na yi kakaki.

"Bana tunanin ina bukatar komai a yanzu. Na shiga siyasa ne saboda Allah ya tsara kuma na samu gogewa sosai a rayuwa," yace.

Ku barni in huta, ba zan nemi kujerar Sanata ba - Masari ga Nagoya bayansa
Ku barni in huta, ba zan nemi kujerar Sanata ba - Masari ga Nagoya bayansa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Abubuwa 6 masu bada mamaki game da Najeriya

A wani labari na daban, jama'ar jihar Katsina na ci gaba da zanga-zanga sakamakon al'amuran rashin tsaro da suka addabi jihar.

Mazauna kauyen 'yan kara da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun rufe manyan hanyoyi tare da kiran dauki daga gwamnati.

Sun zargi gwamnati da nuna halin ko in kula a kan fyade, kashe-kashe da garkuwa da mutane da 'yan bindiga ke yi a yankunan.

Al'amarin ya kawo tsananin cunkoso wanda ya hana masu ababen hawa wucewa a kan babbar hanyar.

Matasan sun dinga yawo da rubutu a manyan fostoci tare da rera wakoki inda suke bukatar kara tsananta tsaro a jihar.

Masu ababen hawa sun dinga sauya hanya sakamakon rufe hanyar da fusatattun matasan suka yi.

Wannan zanga-zangar ta fara ne bayan sa'o'i 24 da 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Faskari tare da halaka a kalla jama'a 40.

A yayin da aka tuntubi DSP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya ce ba zai iya tsokaci a kan lamarin ba saboda bincikar al'amarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel