Korona: Muna cikin mawuyacin hali sosai, in ji Buhari

Korona: Muna cikin mawuyacin hali sosai, in ji Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali a yanzu saboda annobar korona

- Shugaban kasar ya yi jaje ga wadanda suka rasa masoyansu sakamakon cutar da kuma wadanda suka rasa hanyar cin abincinsu saboda matakan gwamnati

- Buhari ya kuma mika godiya ga ma'aikatan lafiya da sauran masu muhimmin aiki da suka ta kokarin ganin an shawo kan lamarin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar wahala sosai sakamakon annobar Coronavirus.

Ya fadi hakan ne a jawabinsa na ranar yancin kai a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni, jaridar The Punch ta ruwaito.

Korona: Muna cikin mawuyacin hali sosai, in ji Buhari
Korona: Muna cikin mawuyacin hali sosai, in ji Buhari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce: “Rana ce ta karrama magabatanmu wadanda suka yi wahala wajen samar da jumhuriyyarmu da duk wani dan Najeriya da ya yi aiki ba ji ba gani domin dorewar ta.

“Muna bikin damokradiyyar wannan shekarar duk da annobar coronavirus wacce ta raunana kasarmu da duniya baki daya.

“Shakka babu wannan lokaci ya kasance mawuyaci ga kowa, musamman wadanda suka rasa masoya sakamakon cutar. Da kuma wadanda suka rasa hanyoyin rike kansu sakamakon tsatsauran matakin da muka shimfida a kowani mataki na gwamnati domin magance annobar da tsare rayuka.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya haramta fita, ya ce kowa ya zauna a gida a inda rikici ya barke

“Sadaukarwar ma’aikatan lafiyarmu da sauran masu muhimmin ayyuka wajen shawo kan wannan cutar ya nuna karfin gwiwarmu a matsayin mutane da kasa mai inganci.

"Kuma na yi amfani da wannan damar wajen mika godiya na ga dukkaninku a kan ayyukanku ga kasar.”

A wani labari na daban, Pauline Tallen, Ministar kula da harkokin mata ta Najeriya ta alakanta hauhawar fyade da dokar kulle da aka saka don dakile yaduwar annobar korona a Najeriya.

Tallen ta sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2020 bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya inda ta kawo matsalar fyade gabansu.

Ta bayyana cewa za a dauka mataki wanda zai hada da na shari'a da kuma kafafen yada labarai don shawo kan matsalar fyade.

A saboda haka muke kira ga kafofin yada labarai don wayar da kai. Ina son mutane su fito su bayyana halin da suke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel