Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

An samu mummunan tashin hankali a majalisar jihar Kaduna a ranar Alhamis yayin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Makera, Dahiru Liman ya kwace sandar majalisar.

Daily Trust ta gano cewa, bayan mintuna kadan da sanar da tsige mataimakin kakakin majalisar, Dan majalisa Dahiru Liman ya shiga zauren majalisar tare da kwatar sandar majalisar don datse al'amarin da ke faruwa.

Amma kuma Dahiru Liman ya sha mugun duka a hannun 'yan majalisar da ke goyon bayan kakakin majalisa, Ibrahim Zailani yayin da ya yi yunkurin ficewa da sandar.

Wakilin Daily Trust da ya ga al'amarin lokacin da yake faruwa ya ce, da kyar sauran 'yan majalisa suka samu damar kwace shi daga hannun masu dukansa yayin da yake kokarin rike sandar.

Daga baya ne sauran 'yan majalisa suka yi kokarin fitar da shi bayan yayyaga kayansa da aka yi kuma jini yana zuba ta hancinsa.

A yayin martani game da harin, Liman ya ce 'yan majalisar 21 ne suka amince da tsigeshi sakamakon rashin iya aiki.

"Mu 'yan majalisa 21 ne muka amince da tsige kakakin saboda rashin kwarewa da jagorantar majalisar.

"Yana haifar da rarrabewar kai tsakanin 'yan majalisa," yace.

Zailani ya musanta dukkan zarge-zarge da ake masa yayin da ya zanta da manema labarai. Ya ce annobar korona ce ta sa ya ki kiran zaman majalisar.

Zaman majalisar yau Alhamis ya samu halartar 'yan majalisa 24 daga cikin 34.

Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)
Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo). Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna)

A ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020 yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun zabi Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani matsayin sabon kakakin majalisar.

An zabeshi ne kimanin awa daya bayan Hanarabul Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus daga kujerar.

Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani wanda ke wakiltar mazabar Igabi ta yamma, ya kasance mataimakin kakain majalisar kafin aka zabesa matsayin Kakaki a ranar Talata.

Zailani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel