An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

- Jami'an hukumar NSCDC sun damke wani mutum da ake zargi da samar wa 'yan Boko Haram kayan bukata

- Mutumin mai shekaru 35 mai suna Bakura Ibrahim an kama shi ne garejin Muna da ke Maiduguri

- Kwamandan NSCDC, Ibrahim Abdullahi daga jihar Borno ne ya tabbatar da wannan ci gaban

Jami'an hukumar NSCDC a jihar Borno sun damke wani mutum da ake zargi da samar wa mayakan Boko Haram kayan bukata.

Kwamandan NSCDC na jihar Borno, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da hakan a garin Maiduguri a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni.

Ya ce an kama mutumin ne da mota dankare da man fetur tare da sauran kayan bukata.

Abdullahi ya ce wanda ake zargin mai suna Bakura Ibrahim ya shiga hannun jami'ai a garejin Muna da ke kan titin Gamboru Ngala da ke Maiduguri a ranar Asabar, 6 ga watan Yuni.

Kayayyakin da aka samu a wurin mutumin mai shekaru 35 sun hada da jarkoki 35 masu cin lita 25 cike da man fetur, kwalin magungunan gargajiya bakwai, jaka 10 ta koma da ragar kamun kifi sai kuma magungunan karin karfin maza.

Kwamandan ya kara da cewa, da hadin guiwar sauran jami'an tsaro sun samu manyan nasarori wurin yaki da barna.

Jami'an NSCDC sun damke mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki
Jami'an NSCDC sun damke mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki
Asali: UGC

KU KARANTA: An kama masu hakar kabari da ke datse kawunan gawarwaki

Kwamandan ya ce hukumar ta yi nasarar damke manyan 'yan ta'addan Boko Haram uku tare da mika su ga rundunar soji don daukar mataki a 2020.

Ya danganta yawaitar hare-haren da 'yan ta'addan ke kaiwa da yawan masu samarwa 'yan ta'addan bayanai, kayan bukata da kuma masoyansu da ke zaune a cikin mutane.

"Hukumar ta tabbatar da cewa hauhawar hare-haren ya samo asali ne daga masu samarwa 'yan ta'addan da kayan aiki. Hakan ne yasa dole a tsananta bincike a tsakankanin jama'a don samun mafita," yace.

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito yadda mayakan Boko Haram suka halaka mutum 70 a ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2020 a jihar Borno.

Mayakan sun kai harin ne a kauyen Faduma Koloram da ke karamar hukumar Gubio ta jihar Borno.

Majiya mai karfi ta tabbatar da cewa maharan sun yi awon gaba da Shanu sama da 300 zuwa 1000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel