Atiku Abubakar ya ba hukumar INEC shawarar gyara kura-kuran 2015 da 2019

Atiku Abubakar ya ba hukumar INEC shawarar gyara kura-kuran 2015 da 2019

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC, da ta gyara kura-kuran da aka samu a zabukan shekarar 2015 da 2019 a zabe mai zuwa na 2023.

Jagoran siyasar adawar kasar ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, 2020. Atiku Abubakar ya yi wannan jawabi ne domin murnar ranar damukaradiyya a Najeriya.

Da ya ke magana ta bakin ofishin yada labarinsa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce akwai matukar bukatar a ‘hanzarta yi wa dokar zabe garambawul’ yayin da ake tunkarar 2023.

Ana kyautata zaton Atiku Abubakar zai sake jarraba sa’ar neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa. Hakan na zuwa ne bayan Adamu Atiku ya fito ya kyankyasa wannan batu kwanaki.

Jaridar Daily Trust ta ce, da Atiku ya ke magana game da siyasar kasar, ya ce akwai bukatar a gyara yadda abubuwa su ke tafiya ta hanyar ganin cewa kuri’un mutane sun yi aiki ne a kan mutanen kwarai.

KU KARANTA: Jam'iyyun siyasa 32 da INEC ta ruguza rajistarsu bayan zaben 2019

Atiku Abubakar ya ba hukumar INEC shawarar gyara kura-kuran 2015 da 2019
Atiku Abubakar
Asali: Twitter

“Daga 1999 zuwa yanzu da aka dawo tsarin mulkin farar hula, siyasar mu ta bada dama ga kowane irin mutum ya samu damar kai wa matakai daban-daban na kujerar mulki.”

“Mafi yawansu, idan ba duka ba, sun yi bakin kokarinsu na ganin sun yi mulki mai inganci a kasar.” Inji Atiku Abubakar.

Sai dai Atiku ya ce: “Sakamakon da su ka samu, daga abin da ake gani a kasa a yau, ya nuna cewa duk kokarin da mu ke yi bai isa ba tukunna.”

“Wajen shawo kan wadannan matsaloli akwai bukatar masu zabe su rika tantance ‘yan takarar da su ka fito – wanda hakan wani romo ne da tsarin farar hula ya kawo ta hanyar zabe a kai - a kai.”

Game da hukuma kuma, Atiku ya ce dole ayi maza a gyara kura-kuran da aka yi a zabukan baya. Wannan ne zai sa kuri’un talakawa ya yi tasari, a kuma inganta kyawun zabe, a cewarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel