Gwamnan Gombe ya yi wa Ali Nuhu ta'aziyar rasuwar mahaifinsa

Gwamnan Gombe ya yi wa Ali Nuhu ta'aziyar rasuwar mahaifinsa

- Gwamna Muhammad Inuwa na jihar Gombe ya yi wa jarumi Ali Nuhu ta'aziyarsu rasuwar mahaifinsa, Nuhu Poloma

- Gwamna Inuwa ya bayyana mamacin a matsayin jarumin dan siyasa, jagoran al'umma kuma dan kishin kasa da za ayi rashinsa

- Ya yi adduar Allah ya jikan marigayin da rahama ya kuma bawa iyalansa ikon jure rashinsa

Gwamnan jihar Gombe, Muhummad Inuwa Yahaya, ya aike da sakon taaziya ga iyalan marigayi Mr Nuhu Poloma da mambobin jami'yyar Peoples Democratic Party, PDP, bisa rasuwar tsohon shugaban jami'yyar na jihar.

Poloma ya rasu ne a ranar Litinin yana da shekaru 78 a duniya.

A sakon ta'aziyar da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya bayyana bakin cikinsa bisa rasuwar marigayi Poloma.

Gwamnan Gombe ya yi wa Ali Nuhu ta'aziyar rasuwar mahaifinsa
Gwamnan Gombe ya yi wa Ali Nuhu ta'aziyar rasuwar mahaifinsa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

Gwamna Inuwa ya bayyana marigayin a matsayin, "Dattijon kirki, jarumin dan siyasa kuma dan kishin kasa da ya yi wa jiharsa da kasarsa hidima a matsayin dan majalisar tarayya a jamhuriya ta biyu, ma'aikacin kwastam, ma'aikacin gwamnati, jigo a jami'yya da jagorar al'umma."

Inuwa ya ce rasuwar Poloma babban rashi ne ga iyalansa, jihar Gombe da Najeriya baki daya.

Ya yi adduar Allah madaukakin sarki ya gafarta masa da rahama ya kuma bawa iyalansa ikon jure rashin sa.

Paloma ne mahaifin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu.

A bangarensa, Ali Nuhu ya mika godiyarsa ga magoya bayansa bisa adduoin da suka masa tun bayan rasuwar mahaifinsa.

Jarumin ya yi amfani da shafinsa na Instagram a ranar Laraba ya wallafa sako kamar haka.

“Ni da yan’uwana muna mika sakon godiya ga dukkan wadanda suka yi Mana ta’aziyyar mahaifinmu da ya rasu. Mungode Allah ya saka da alheri. Na gode da soyayya da kaunar da na samu daga gareku gaba daya, Allah ya bar zumunci.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel