Harkallar filaye: Tubabben sarkin Kano Sanusi II ya daukaka kara

Harkallar filaye: Tubabben sarkin Kano Sanusi II ya daukaka kara

- Tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta yanke hukunci a kan halascin bincikarsa kan harkallar filaye

- Lauyoyin tsohon sarkin sun ce a matsayinsu na masu wakiltarsa, ba a sanar da su ranar yanke hukuncin ba

- Saboda haka suka shawarci Sanusi II ya daukaka kara

Tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta yanke hukunci a kan halascin bincikarsa da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ke yi a kan harkallar filaye, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda tubabben sarkin ya bayyana ta hannu lauyansa, ya ce: "A ranar 8 ga watan Yunin 2020, babbar kotun tarayya da ke zama a Kano karkashin jagorancin Jastis Lewis- Allagoa, ya tabbatar da cewa binciken bai take wani hakki na tubabben basaraken ba."

Harkallar filaye: Tubabben sarkin Kano Sanusi II ya dauka kara
Harkallar filaye: Tubabben sarkin Kano Sanusi II ya dauka kara Hoto: Pulse.ng
Asali: UGC

Lauyoyin basaraken sun kara da cewa, "A matsayinmu na masu wakiltarsa, ba a sanar da mu ranar yanke hukuncin ba. Amma mun samu takardar shari'ar a ranar 10 ga watan Yunin 2020 kuma mun yi nazarinta.

"Mun ba wa mai martaba shawarar daukaka kara. A ranar 10 ga wata mun shigar da kara mai kalubalantar hukuncin babban kotun tarayyar da ta yanke a ranar 8 ga watan Yunin 2020.

"Muna fatan kotun daukaka kara ta duba al'amarin."

KU KARANTA KUMA: Rikicin kabilanci: Rayuka masu tarin yawa sun salwanta a Adamawa

Da farko dai mun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin ta kori karar da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wacce ke bukatar dakatar da bincikar zargin wata almundahanar filaye da masarautar jihar Kano ta yi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris din 2020 ne tsohon basaraken ya tunkari kotun da bukatar cewa a dakatar da Ganduje, antoni janar da kuma shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

Korafin ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano da shugabanta, Muhyi Rimingado, da ya dakata da bincikarsa har sai an kammala shari'ar farko.

Alkali mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ya yanke hukuncin cewa, hukumar ba ta take wani hakki na tsohon basaraken ba na bincikarsa a kan zargin da ake masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel