Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'addan suna tsaka da taro

Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'addan suna tsaka da taro

Rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta kashe 'yan ta'addan Boko Haram tare da tarwatsa maboyarsu da ke Kacha Korle a dajin Sambisa na jihar Borno.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Kamar yadda yace, sun yi wannan aikin ne a ranar 10 ga watan Yuni bayan bayanan sirrin da suka samu da ke nuna inda mayakan kungiyar ta'addan ke yin taro.

Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'adda suna taro
Boko Haram: Rundunar soji ta ragargaza 'yan ta'adda suna taro Hoto: Channels Television
Asali: UGC

Enenche ya tabbatar da cewa mayakan na boyewa a dajin inda suke shiryawa tare da aiwatar da hari ga farar hula da sojin. Daga nan ne suke shiryo duk wani harin da za su yi a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, Channels Television ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade

"Yadda ya dace, jiragen yaki sun kai samame maboyarsu tare da ragargazasu.

"An yi nasarar halaka mayakan Boko Haram masu tarin yawa tare da tarwatsa maboyar," takardar tace.

Shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya jinjinawa dakarun tare da kira garesu da su tsananta hana 'yan ta'addan sakat.

A wani ci gaba makamancin hakan, hedkwatar tsaro ta jinjinawa kwazo da jajircewar sojojin sama da sauran jami'an tsaro tare da masu ruwa da tsaki a kan yadda suke kokarin kawo karshen Boko Haram."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya bada umarnin ga dakarun da su binciko tare da halaka 'yan bindigar da suka addabi Katsina.

Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis da ya gabata inda ya umarcesu da mika rahoton ayyukansu na kowanne mako.

A yayin ziyara da ya kai wa rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina, Abubakar ya ce, "Dole ne mu nemo inda 'yan bindigar suka boye tare da halaka su.

"Kada mu saurara har sai jama'a sun koma yadda suke a da ba tare da tsoron hari daga 'yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba," yace.

Ya ce za a samar da dukkan kayayyakin da dakarun ke bukata don ba za a bar 'yan bindigar su numfasa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng