Akwai bukatar a tallafawa wasu Jihohi da Yankin Arewa maso Gabas da $182m - WFP

Akwai bukatar a tallafawa wasu Jihohi da Yankin Arewa maso Gabas da $182m - WFP

- UN za ta taimakawa Jihohin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya ci

- Haka zalika za a tallafawa Kano, Legas da Abuja inda COVID-19 ta yi kamari

- Mutum akalla 8, 000 ne Coronavirus ta harba tsakanin Kano, Legas da Abuja

Jaridar The Guardian ta ce Majalisar dinkin Duniya ta na kokarin hadawa miliyoyin mutanen Najeriya da annobar cutar COVID-19 ta shafa gudumuwa na musamman.

Majalisar dunkin Duniyar za kuma ta bada agaji ga mutanen yankin Arewa maso gabas da su ke cikin wani mawuyacin hali a sakamakon yakin Boko Haram da ake ta yi.

Hukumar Duniyar za ta taimakawa Najeriya ne da fam Dala miliyan 182. Idan aka yi lissafi a kudinmu na gida, wannan gudumuwa za ta kai kimanin Naira biliyan 70.3.

A cewar hukumar WFP, wadannan makudan kudi za su yi amfani na tsawon watanni shida ana ba ‘yan Najeriyar da wannan annobar cuta da kuma matsalar tsaro ta shafa.

KU KARANTA: Za a koma karatu a Makarantun Gwamnati a K/Riba - Gwamna

Za a tallafawa wasu Jihohi da Yankin Arewa maso Gabas da $182 - WFP
Elisabeth Byrs Hoto: Andalolu Agency
Asali: Twitter

Mutane miliyan uku da ke yankin Kano, Abuja, da Legas za a kawowa dauki da wannan kudi, baya da irin kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi a manyan biranen kasar.

Mai magana da yawun bakin hukumar WFP ta Duniya, Elisabeth Byrs, ta koka da yadda mutanen yankin Borno, Yobe da kuma Adamawa su ke fama da yunwa a halin yanzu.

Wadannan jihohi uku su ne inda rikicin ta’addancin Boko Haram ya fi yi wa tasiri a Najeriya.

A wani jawabi da Elisabeth Byrs ta fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2020, ta ambaci wadannan jihohi a matsayin inda su ka fi bukatar taimako a yankin Tafkin Chadi.

Akwai mata da kananan yara fiye da miliyan 7.9 da su ke matukar bukatar agaji.

Legas, Kano da Abuja kuma su ne jihohin da aka fi samun barkewar cutar Coronavirus. Akwai fiye da mutane 8, 300 da su ka kamu da COVID-19 kawo yanzu a wadannan garuruwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng