Stella Oduah: Lauyoyin EFCC za su gangara zuwa kotun daukaka kara a Najeriya

Stella Oduah: Lauyoyin EFCC za su gangara zuwa kotun daukaka kara a Najeriya

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta yi tir da wani hukunci da kotu ta yanke a kanta, inda ta sha alwashin neman nasara a kotun gaba.

EFCC ba ta gamsu da hukuncin da aka yi mata a shari’ar ta da Sanata Stella Oduah ba, inda Alkali ya bada umarnin cewa a maida mata duk wasu kadarorinta da gwamnati ta karbe.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa za ta kalubalanci wannan hukunci a gaban kotun daukaka kara.

Alkalin wani babban kotun tarayya da ke Abuja ne ya bukaci hukumar EFCC ta maidawa tsohuwar ministar harkokin jirgin saman Najeriya watau Stella Odua dukiyoyinta da ta rike.

Mai magana da yawun bakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya nuna rashin gamsuwarsu da yadda shari’ar ta kaya, ya tabbatar da cewa za su tafi wajen Alkalan kotun daukaka kara.

“Hankalin EFCC ya je ga wani hukunci da babban kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar Litinin, na yunkurin karbe dukiyoyin da ke hannun tsohuwar ministar harkokin jiragen sama, Sanata Stella Oduah.” Inji Mista Dele Oyewale.

KU KARANTA: Zan karbo kujerata a gaban kotun daukaka kara - Dino Melaye

Oyewale ya kara da cewa: “Alkali Inyang Ekwo, a hukuncinsa, ya yi fatali da karar EFCC, da sunan cewa an gabatar da rokon kafin a nemi kotu ta bada karin lokacin shigar da karar.”

“EFCC ba ta gamsu da hukuncin wannan sharia ba, kuma za ta daukaka kara a kotu na gaba.”

Dele Oyewale ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja.

Ana zargin sanatar Anambra ta Arewa, Stella Oduah da karkatar da wasu Naira biliyan 9.5 da aka ware domin shigo da kayan aiki a filayen jirgin saman Najeriya a gwamnatin Jonathan.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa EFCC ta yi nasarar daure wasu mutum tara da aka samu da laifin damfara. Kotun tarayya da ke Abeokuta ta yanke masu hukuncin dauri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel