Ba shakka PDP za ta kwace jihar Edo - Fintiri

Ba shakka PDP za ta kwace jihar Edo - Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri ya ce jam'iyyar PDP za ta karbe shugabanci a zabe mai zuwa na gwamnonin jihar Edo.

Ya ce kamar yadda ya bayyana a zabukan PDP da suka gabata tare da halin da jihar Edo ke ciki a yanzu zai assasa aukuwar hakan.

Fintiri, wanda shine shugaban kwamitin PDP ya sanar da hakan ne a Benin yayin da jam'iyyar ke taron zaben wakilai don zaben fidda gwani da ke gabatowa.

"Ba tare da hada zance ba, ina so in ce jihar Edo ta PDP ce saboda a zabukan baya, kun ga kokarinmu, mun yi kokari sosai, mun lashe zaben shugaban kasa a nan Edo, mun lashe kujerun sanatoci biyu cikin uku, kujerun majalisar wakilai hudu cikin biyar a jihar.

"Mun zo yin muhimmin aiki ne a jihar nan don samun fitar da wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyarmu mai albarka."

Ba shakka PDP za ta kwace jihar Edo - Fintiri
Ba shakka PDP za ta kwace jihar Edo - Fintiri Hoto: Breaking Times
Asali: Facebook

Ya bukaci zababbun wakilan jam'iyyar da su yi zabe cikin hikima don zabar dan takara da ya cananta wanda zai iya kawowar jam'iyyar nasara a zaben gwamna mai zuwa a jihar.

KU KARANTA KUMA: Mu na fuskantar hantara da cin zarafi a filayen jirgi - Sadiq Abacha

Ya yi kira ga wakilan jam'iyyar da su dage wajen tsayawa kan ra'ayin jama'ar jihar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, kwamitin ya samu shugabancin Fintiri , gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri da Sanata Sam Ayanwu.

A gefe guda mun ji cewa jam'iyyar APC ta fara tantance 'yan takararta shida da ke neman tikitin fitowa neman kujera gwamnan jihar Edo a ofishin jam'iyyar da ke Abuja a yau Laraba.

Shugaban kwamitin tantancewar, Farfesa Jonathan Ayuba, ya ce a yau tantance takardu kadai za su yi tare da mika rahoton aikinsu gaban jam'iyyar.

'Yan takara uku ne suka bayyana don tantancewar.

Sune Osaro Obaze wanda ya fara mika kansa don tantancewar sai Gwamna Godwin Obaseki da ya bayyana wurin karfe 1 da goma sannan ya tafi bayan minti biyar.

Injiniya Chris Ogiemwonyi ya halarci wurin tantancewar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel