Dabiu'u 10 na yau da kullum da ke illata kwakwalwa
Duk da kasancewar kwakwalwa halitta mai matukar muhimmanci a jikin mutum da dabba, ba kowa ke damuwa da abubuwan da kwakwalwa ke bukata domin yin aikinta da kyau ba.
Riko da wasu dabiu'u da kuma gujewa wasu dabiu'u zai taimaka wajen hana lalacewar kwakwalwa tare da inganta lafiyarta.
Ga duk mai son kwakwalwarsa ta kasance cikin koshi lafiya ya kamata ya guji wadannan dabi'u guda 10:
1. Tsallake kumallon safe
Kwakwalwa tana bukatar wasu sinadaran abinci a lokutan da suka dace.
Saboda yawan harkokin rayuwa, jama'a da dama basa karyawa da safe, wanda hakan ke haddasa karancin sinadrin 'glucose' da kwakwalwa ke matukar bukata domin samun karfin aiki.
2. Karancin bacci
Rashin samun isashen bacci yana hana kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata. Rashin samun wadataccen bacci yana haddasa tabarbarewar kwakwalwa wajen rike abu.
Karancin bacci na jawo mutuwar wasu halittu a cikin kwakwalwa, lamarin da ke haddasa matsananciyar mantuwa, misali; manta hanya, manta makullai da kasa tuna wurin da mutum ya yi ajiya.
Domin gujewa irin wannan tabarbarewar kwakwalwa, masana sun bayar da shawarar samun baccin sa'a 7 a kowacce rana.
3. Cin abincin da ya wuce kima
Cin abincin da ya wuce misali yana hana kwakwalwa ta yi aiki da kyau. Cushe ciki da abinci yana jawo shigar maiko cikin jijiyoyin da ke kai jini cikin kwakwalwa tare da kumburasu, lamarin da ke haddasa karancin jini a cikin kwakwalwa.
Kwakwalwa ba ta iya aiki yadda ya kamata idan akwai karancin zuwan jini cikinta. Bayan haka, cika ciki da abinci yana haddasa wasu sauran wasu cututtuka daban - daban.
4. Ci da shan abubuwa masu yawan sukari
Cikin rashin sani ko sabanin haka, mutane na yawan dirkar kayan abinci da na sha masu dauke da sukari.
Yawan cin kayan zaki da aka sarrafa da tataccen sukari yana hana tace sinadaran da kwakwalwa ke aiki da su, lamarin da kan iya haifar da matsalolin kwakwalwa irinsu rawar kai da susucewa.
DUBA WANNAN: Bayan haihuwar 'yan uku sau biyu a baya; uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria
5. Shan hayaki
Wannan ita ce babbar dabi'ar da mutane suka runguma wacce ke lalata kwakwalwa da sauran halittun jikin da suka hada da hunhu da zuciya.
Yawan shan hayaki yana haddasa kankancewar kananan halittun cikin kwakwalwa, wanda hakan ke haifar da cututtukan da zasu iya sanadin mutuwar mutum gaba daya.
6. Rufe fuska yayin kwanciya bacci
Yayin da mutum ya rufe kansa idan ya kwanta bacci, ya takaita fitar gurbatacciyar iskar da yake fitarwa daga jikinsa da kuma shan iska mai kyau.
Karancin samun iska mai kyau yana rage gardin bacci tare da rage karfin kwakwalwa.
7. Rashin motsa jiki
Ba iya kwakwalwa motsa jiki ke amfana ba, yana taimakon zuciya da hunhu, sannan yana hana saurin tsufa da takwarkwashewa.
8. Kwankwadar barasa
Yawan shan giya, yawan kananan halittun kwakwalwa da zasu mutu, a cewar masana.
Yawan kwankwadar barasa yana haifar da raguwar farin sinadarin da ke cikin kwanya.
9. Sauraron kida a kure murya yayin da aka saka kananan lasifikun kunne
Ba iya halittun cikin kunne ne ke samun matsala ba idan mutum yana sauraron kida bayan ya kure murya yayin da ya saka kananan lasifikun kunne ba.
Hakan yana shafar har kwakwalwa, saboda ita ce ke aikin tantance duk wani abu da mutum ya ji ko ya gani. Kure sautin murya ya na takura kwakwalwa, lamarin da, tabbas, zai haddasa sukurkucewarta.
10. Yawan aiki ba hutawa
Duk da dabi'ar aiki tukuru, dabi'a ce mai kyau, yin aiki fiye da karfin mutum babbar matsalace ga lafiyar kwakwalwarsa da jikinsa.
Idan mutum yana yawaita yin aiyukan da suka fi karfinsa, zai ji kwakwalwarsa ta yi nauyi, yana yawan fushi da kunci, sannan ya kasa bacci.
Idan mutum ya fara jin irin wadannan alamu, ya kamata ya tuntubi masana domin neman shawara.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng