Da duminsa: Obaseki da 'yan takara biyu sun bayyana a sakatariyar APC don tantancewa
- Jam'iyyar All Progressives Congress ta fara tantance 'yan takararta da ke neman tikitin fitowa neman kujera gwamnan jihar Edo
- 'Yan takara uku iki harda Gwamna Godwin Obaseki ne suka bayyana don tantancewar
- Shugaban kwamitin tantancewar, Farfesa Jonathan Ayuba, ya ce a yau tantance takardu kadai za su yi tare da mika rahoton aikinsu gaban jam'iyyar
Jam'iyyar APC ta fara tantance 'yan takararta shida da ke neman tikitin fitowa neman kujera gwamnan jihar Edo a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja a yau Laraba.
Shugaban kwamitin tantancewar, Farfesa Jonathan Ayuba, ya ce a yau tantance takardu kadai za su yi tare da mika rahoton aikinsu gaban jam'iyyar.
'Yan takara uku ne suka bayyana don tantancewar.
Wadannan yan takara sune Osaro Obaze wanda ya fara mika kansa don tantancewar sai Gwamna Godwin Obaseki da ya bayyana wurin karfe 1 da goma sannan ya tafi bayan minti biyar.
KU KARANTA KUMA: Mu na fuskantar hantara da cin zarafi a filayen jirgi - Sadiq Abacha
Injiniya Chris Ogiemwonyi ya halarci wurin tantancewar.
A wani labari na daban, jami'ar jihar Ibadan ta tabbatar da cewa Injiniya Gwamna Godwin Obaseki tsohon dalibinta ne.
A takardar da rijistiran makarantar, Olubunmi Faluyi ta fitar, ta ce Godwin Nogheghase Obaseki tsohon dalibinta ne.
Kamar yadda takardar ta bayyana, Gwamnan ya samu gurbin karatu a makarantar a shekarar 1976 kuma ya kammala a 1979.
"Bayanai a kan karatunda da kammala suna kammale a tare da jami'ar," takardar tace.
Wasu shugabannin APC sun zargi Obaseki da gabatar da satifiket din bogi daga jami'ar.
Wannan takardar daga jami'ar ce za ta janye wannan zargin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng