Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari

Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari

A ranar Laraba, majalisar dattawan Najeriya ta musanta umartar hukumar yaki da rashawa (EFCC) da bincikar ministan harkokin yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio.

A kwanakin baya an yada wata wasika da majalisa ta umarci EFCC ta binciki Akpabio a kan harkallar kudaden hukumar kula da al'amuran yankin Neja Delta NDDC.

Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ovie Omo-Agege ya barranta majalisar da wannan wasikar.

Hakazalika, a ranar Laraba, magatakardan majalisar dattawa, Nelson Ayewoh a wata takarda da ya fitar a Abuja, ya tsame hannun majalisar dattawan daga fidda wannan wasikar.

Ya bukaci jama'a da su yi watsi da wannan wasikar don ta bogi ce.

Takardar ta bayyana: "Hankalina ya kai ga wata wasikar bogi mai kwanan wata 7 ga Mayun 2020 wacce aka yi ikirarin ta fito daga ofishina zuwa EFCC.

"Kamar yadda wasikar bogin ta bayyana, mataimakin majalisar dattawa ya umarci magatakardar majalisa da ya mika koke don bincikar ministan kula da harkokin Neja Delta a kan zargin almundahana.

"Tuni ofishin mataimakin majalisar dattawa ya yi martani a kan wannan wallafar da koken na bogi.

Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari
Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari. Hoto daga Pulse.ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur

"Na matukar yarda da abinda mataimakin shugaban majalisar ya fitar na cewa takardar ta bogi ce mai fatan haddasa gaba, karya da rashin zaman lafiya.

"Bugu da kari, ana bukatar dukkan jama'a da kuma wadanda abun ya faru da su kiyaye abubuwa kamar haka:

"Cewa babu wani lokacin da mataimakin shugaban majalisar, Sanata Augustine Ovie Omo-Agege, ya miko min wani koke da ya danganci wata cibiyar gwamnati."

A wani labari na daban, Sanata Peter Nwaoboshi ya yi barazanar maka mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Lauretta Onochie a gaban kuliya.

Nwaoboshi ya yi wannan barazanar ne tun kafin majalisar dattawa ta ba jami'an tsaro damar bincikar zargin takardar bogi da aka fitar daga mataimakin shugaban majalisar a kan bincikar ministan yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio.

A wata wasika da Nwaoboshi ya fitar ta hannun lauyansa, ya bai wa hadimar sa'o'i 48 da ta janye tsokacin da ta yi a kan kwangilar yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel