COVID-19: FG ta yi asarar N1.01tn a kudin shiga

COVID-19: FG ta yi asarar N1.01tn a kudin shiga

Mummunar illar annobar korona ta ja wa gwamnatin tarayya asarar kusan tiriliyan 1.01 a watanni uku na farkon shekarar nan.

Faduwa a kudin shigar, kamar yadda wata takarda da ta bayyana daga the whistler.ng wacce tace ta fito daga ofishin kasafin tarayya ne, an gano cewa hakan ta faru ne saboda faduwar da raguwar kudin shiga da ke shigewa asusun tarayya.

Annobar ta kara da kawo faduwar farashin danyen man fetur a fadin duniya.

COVID-19: FG ta yi asarar N1.01tn a kudin shiga
COVID-19: FG ta yi asarar N1.01tn a kudin shiga Hoto: The Cable
Asali: UGC

Barkewar muguwar cutar ta korona ya janyo dokar hana walwala a jihohi daban-daban na fadin kasar nan, ci gaban da ya gurgunta al'amuran tattalin arziki.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A misali, daga cikin N1.96 tiriliyan da gwamnatin tarayya ta yi tsammanin samu na kudin shiga a watanni ukun farkon shekarar nan, ta samu N950.55 biliyan.

Idan aka dogara da kiyasin kudin shigar, faduwar da asarar N1.01 tiriliyan na nuna asarar kashi 52 na kudin shiga.

Game da dukkan kudin shiga, annobar ta taka rawar gani wurin kawo asarar kashi 30 daga N659.4 da aka yi kiyasin samu.

Kudin shigar da aka samu a cikin watanni uku a bangaren man fetur shine N464.03 biliyan.

Hakazalika, an ga illar annobar a bangaren iskar gas da aka yi kiyasin samun N31.07 biliyan.

A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya ce idan annobar COVID-19 ta ci gaba, a kalla 'yan Najeriya miliyan 20 ne za su rasa aikinsu.

KU KARANTA KUMA: Sai dai ku ƙarata, amma babu gudu babu ja da baya a kan sabuwar doka ta 10 - Buhari ya fadawa Gwamnonin Najeriya

Lawan ya kara da cewa, siyasar kasa da kasa ke hana Najeriya samar da makaman zamani don amfanin rundunar soji wajen fatattakar rashin tsaro.

A yayin jawabi ga manema labarai a garin Abuja yayin shirye-shiryen bikin zagayowar shekara na majalisar, Lawan ya ce duk lokacin da Najeriya ta bukaci siyan makamai daga kasashen ketare, ana daukar tsawon lokaci kafin a aminta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel