Saboda kokarin da Danbatta ya yi, na bukaci ya kara shekara 5 a NCC – Inji Pantami
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ibrahim Ali-Pantami, ya bayyana dalilinsa na ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar sake nada farfesa Umar Danbatta a matsayin shugaban hukumar NCC.
Isa Ibrahim Ali-Pantami ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin hukumar NCC su ka kawo masa ziyarar ban girma a ofishinsa. Ministan ya ce ya dauki matakin hakan ne domin ganin abubuwa sun daure a ma’aikatar.
Mai girma ministan ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020 kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Nigerian.
Dr. Isa Ibrahim Ali-Pantami ya kuma bayyana cewa matakin da ya dauka ya na da nasaba da nasarorin da harkar sadarwa ta samu a cikin shekaru biyar da su ka wuce a dalilin kokarin da Umar Danbatta ya yi a hukumar NCC.
Duk da haka Pantami, ya yi magana game da bukatar shugabannin NCC su hada-kai su yi aiki tare da ma’aikatarsa da sauran hukumomi wajen ganin an cin ma burin da gwamnati ta yi niyya na NDEPS tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.
KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya sake nada Danbatta a matsayin Shugaban NCC

Asali: Twitter
Ministan ya kuma tunawa shugaban NCC cewa abin da ake bukata wurinsa shi ne ya bunkasa hanyoyin sadarwa da tattalin arzikin zamani, wanda bukatar hakan ta fi muhimmanci a yanzu bayan barkewar annobar cutar COVID-19.
“Nasarorin hukumar sun rataya ne a kan mu gaba daya. Yayin da mu a matsayinmu na ma’aikata, za mu yi bakin kokarinmu na kawo tsare-tsare, sannan kuma mu sa ido a kan ayyukan hukumar.”
An rahoto Dr. Pantami ya cigaba da cewa: “Ina kira ga gidan NCC su hada-kai, su ajiye duk bambanci, su tabbatar da adalci da gaskiya wajen duk matakan da za su dauka. Bugu da kari, su samu hadin-kai.”
Wadanda su ka takewa Danbatta baya sun hada da: Ubale Maska, Adewolu; Shu’aibu Ayuba; Yetunde Akinloye; Efosa Idehen. Sai kuma Dr. Henry Nkemadu; Mohammed Babajika, da Usman Mala.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng