EFCC: Kotu ta bada umarnin rike N827, 679, 098 da ke hannun wani Mutumi

EFCC: Kotu ta bada umarnin rike N827, 679, 098 da ke hannun wani Mutumi

A jiya ne babban kotun tarayya da ke zama a Legas ya zartar da hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta karbe wasu Naira miliyan 827 daga hannun Mista Matthew Edevbie.

A ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, 2020 ne Alkali mai shari’a Chukwujeku Aneke ya yanke wannan hukunci bayan karar da wani lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya kawo gabansa.

Rotimi Oyedepo ya zargi wannan mutumi, Matthew Edevbie wanda ‘dan kasuwa ne da mallakar makudan kudi N616, 679, 098.32 da wasu N211, 000, 000.00 ta kazamar hanya.

Hukumar EFCC ta ce akwai alamar tambaya game da yadda Matthew Edevbie ya samu N827, 679, 098.32, don haka ta nemi kotu ta sa takunkumin taba wadannan makudan kudi.

“Ana zargin an mallaki kudin ne ta kazamar hanya wanda hakan ya sabawa sashe na 17 na dokar damfara da sauran makamantan laifffuka na shekarar 2006.” Inji lauyan EFCC.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

EFCC: Kotu ta bada umarnin rike N827, 679, 098 da ke hannun wani Mutumi
Babban kotu a Najeriya
Asali: Depositphotos

Oyedepo ya kuma shaidawa kotu cewa laifin da ake zargin ‘dan kasuwar da aikatawa ya sabawa sashe na 44 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya roki a karbe miliyoyin.

EFCC ta ce an ajiye wadannan kudi ne a cikin asusun kamfanin Flank Power Ltd kamar yadda jaridar This Day ta bayyana. Hukumar ta kuma samu nasarar farko a wannan karan.

A zaman, Alkali Aneke ya yi na’am da wannan roko na hukumar EFCC bayan ya saurari karar. Alkalin ya umarci gwamnatin tarayya ta rike wannan kudi kafin a kammala shari’ar.

Kotu ta bukaci EFCC ta shiga gidan jarida ta yi cigiyar masu neman kare wannan kamfani da su bayyana a kotu nan da kwana 14 domin hana a karbe wannan miliyoyi na din-din-din.

Binciken da mu ka yi ya nuna mana cewa Matthew Edevbie ‘dan kasuwa ne wanda ya dade ya na harkar wutar lantarki a Najeriya, kuma shi ne mai kamfanin nan na Income Electrix.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng