Dalilinmu na kafe bayanan 'yan takarar gwamnan Edo a allon bango - APC

Dalilinmu na kafe bayanan 'yan takarar gwamnan Edo a allon bango - APC

Jam'iyyar APC ta ce ta kafe bayanan dukkan 'yan takararta da suka sayi fom domin neman takarar kujerar gwamnan jihar Edo saboda kaucewa abinda ya faru a zaben kujerar gwamnan jihar Bayelsa.

An kwace kujerar gwamnan jihar Bayelsa daga hannun jam'iyyar APC tare da damkawa jam'iyyar PDP.

Kotun koli ce ta zartar da hukunci bayan samun wasu kura - kurai a takardun karatun dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar APC.

Jam'iyyar APC ta like bayanan takardun karatun 'yan takararta 6 da suka hada da gwamna Godwin Obaseki, Fasto Osagie Ize-Iyamu, Dakta Pius Odubu, Injiniya Chris Ogiemwonyi, Honarabul Osaro Obazee da Honarabul Matthew Aigbuhuenze Iduoriyekemwen.

Mallam Issa - Onilu, sakataren yada labaran jam'iyyar APC, ya ce, "mun dauki wannan mataki ne sakamakon darasin da muka koya daga abinda ya faru a jihar Bayelsa.

"Mun yi bakin kokarinmu a wancan lokacin, amma duk da haka an samu matsala. Shi yasa muka dauki wannan mataki, saboda wasu zasu iya ganin kuskuren da hankalinmu bai kai kansa ba."

Jam'iyyar APC ta tsayar da ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata gudanar da zaben cikin gida domin fidda wanda zai mata takarar kujerar gwamna a jihar Edo.

Har yanzu ba a cimma matsaya dangane da yanayin zaben fidda gwarzon dan takarar gwamnan APC na jihar Edo ba, lamarin da ke ci gaba da kawo cece-kuce.

Dalilinmu na kafe bayanan 'yan takarar gwamnan Edo a allon bango - APC
'yan takarar gwamnan Edo a allon bangon jam'iyyar APC
Asali: Twitter

A yayin da kwamitin zartarwa na uwar jam'iyyar APC ya aminta da salon zaben kato bayan kato, inda duk mai shaidar zama dan jam'iyya zai iya yin zaben dan takarar da yake so.

Magoya bayan Gwamna Godwin Obaseki ba su aminta da hakan ba. Sun fi son wakilan jam'iyyar su fito don yin zaben.

Gwamna Obaseki na ta rokon fadar shugaban kasa da ta soke hukuncin kwamitin zartarwar jam'iyyar.

KU KARANTA: 2023: PDP ta mayar da martani a kan yiwuwar sake samun takara a wurin Atiku

An gano cewa fadar shugaban kasar ta shiga halin tsaka mai wuya a kan wannan al'amari.

Baraka a kan yanayin zaben fidda gwanin ya kai ga zargin cewa bangaren shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na tsananta yakin neman kada Obaseki.

Shugaban jam'iyyar APC na Edo ta tsakiya, Chief Francis Inegbeniki, wanda yake na hannun daman Adams Oshiomhole, ya tattara laifuka 50 na Obaseki wadanda sun isa su hana gwamnan zarcewa.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar ba su amince da Obaseki da mataimakinsa ba saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da shugaban jam'iyyar tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel