Edo: Kofofinmu a bude suke ga fusatattun mambobin APC - PDP

Edo: Kofofinmu a bude suke ga fusatattun mambobin APC - PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nuna shirinta na karban gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da sauran fusatattun mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) hannu bibbiyu idan suka yanke shawarar dawowa cikinta.

Babban sakataren labaran jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbodiyan, ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni.

Sai dai kuma jam’iyyar ta ce duk wadanda ke da burin dawowa tafiyarta ya zama dole su shirya kansu don bin ka’idoji da dokokin PDP.

Ologbodiyan ya kuma bayyana rade-radin da ake na cewa jam’iyyar ta nemi makudan kudade daga Obaseki yayinda yake shirin sauya sheka a matsayin mara tushe balle makama, jaridar Punch ta ruwaito.

Edo: Kofofinmu a bude suke ga fusatattun mambobin APC - PDP
Edo: Kofofinmu a bude suke ga fusatattun mambobin APC - PDP Hoto: Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya ce: “A karkashin jagorancin Prince Uche Secondus a matsayin Shugaban PDP na kasa, bama yarjejeniya kan kujerun siyasa, bama siyar da kujerun siyasa. A bayyane yake, kuna iya bincikawa. Abun mamaki ne wani ya yi irin wannan zargin.

“Ban taba zama a kowani taro da aka tattauna wannan lamari da ake zargi ba. Zargin bai da tushe kuma ba abun yarda bane garemu a matsayinmu na jam’iyya.

“Ina sane da cewar PDP na da yan takara a jihohin Edo da Ondo.

“Kafin fadawa halin da ake ciki a Edo, jam’iyyarmu a bude take kuma duk wani dan Najeriya da ke shirin takara a zaben fidda gwani na gaskiya da damokradiyya yana da yancin dawowa jam’iyyar.”

KU KARANTA KUMA: Kaduna: An kashe matasa 4 da ake zargi da zama 'yan leken asiri

Ya kuma ci gaba da bayanin cewa PDP na da tarin mambobi da suka cancanci takarar zabukan gwamna a jihohin Edo da Ondo.

A baya mun ji cewa Dan takarar kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, Kenneth Imasuagbo ya ce yana da tabbacin cewa zai yi nasara a zabe mai zuwa. Ya yi ikirarin cewa "Ubangiji ya sanar da ni hakan."

Ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi yayin da gidan talabijin din Channels ya karba bakuncinsa a shirin Sunday Politics.

Kamar yadda yace, Ubangiji ya sanar da shi cewa zai zama gwamnan jihar Edo kuma babu wanda ya isa ya hana cimma wannan burin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel