Yanzu-yanzu: Sakataren gwamnatin jihar Nasarawa ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Sakataren gwamnatin jihar Nasarawa ya yi murabus

- Alhaji Ahmed Tijjani Aliyu ya yi murabus a matsayin sakataren gwamnatin jihar Nasarawa

- Aliyu ya yi murabus ne bayan kwanaki kadan da majalisar jihar ta bukaci ya sauka daga matsayinsa

- Kafin ya yi murabus, jami'an gwamnatin jihar sun bincikesa a kan zarginsa da suke da waskar da wasu kudade

Wani rahoto daga jaridar Daily Sun ya bayyana cewa sakataren gwamnatin jihar Nasarawa, Alhaji Ahmed Tijjani Aliyu ya yi murabus.

Sakataren gwamnatin jihar ya yi artabu da 'yan majalisar jihar Nasarawa.

Aliyu ya yi murabus ne bayan kwanaki kadan da 'yan majalisar dokokin jihar suka bukaci ya sauka daga kujerarsa a kan harkallar kudaden wasu ayyuka har naira miliyan 284.5 tun lokacin yana kwamishinan ilimi.

Yanzu-yanzu: Sakataren gwamnatin jihar Nasarawa ya yi murabus
Yanzu-yanzu: Sakataren gwamnatin jihar Nasarawa ya yi murabus Hoto: The Sun
Asali: UGC

Majalisar ta bukaci ya yi murabus ne bayan tattaunawar da kwamitin ya yi a kan rahoton da aka samu.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Masu nazarin siyasa a jihar Nasarawa sun ce akwai yuwuwar sakataren gwamnatin na daga cikin masu juya mulki a jihar.

A yayin martani a kan murabus din, magoya bayan tsohon sakataren gwamnatin jihar sun dinga jinjina masa a kafafen sada zumuntar zamani.

Duk da magoya bayan tsohon sakataren gwamnatin jihar na nuna bukatarsu na son zamansa gwamnan na gaba, gwamna Sule ya ce bai damu da zarcewa ba a 2023.

Gwamna Sule ya ce yana godiya ga Allah da ya ba shi damar mulkar jihar na shekaru hudu. Ya ce hakan ya isa ya bada gudumawarsa a ci gaban jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a kan batun tazarcensa.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a lafiya yayin taro da kwamitin yaki da cutar na jihar ta gudanar.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, cike da alhini yake sanar da mutuwar mutum hudu wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma daga cikin mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng