Komawar Buratai yankin arewa maso gabas ya sauya al'amura da yawa - Ndume

Komawar Buratai yankin arewa maso gabas ya sauya al'amura da yawa - Ndume

Sanata Ali Ndume, ya ce komawar shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai yankin arewa maso gabas ya taka babbar rawa wajen durkusar da ta'addancin 'yan Boko Haram.

Ndume, wanda shine shugaban kwamitin kula da al'amuran sojin kasar nan a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a garin Maiduguri a yau Litinin yayin tattaunawa da manema labarai.

Ya ce da yawa daga cikin nasarorin da aka samu an same su ne cikin watanni biyun da Buratai ke yankin. A halin yanzu, karashe ya rage a yankin tafkin Chadi, dajin Sambisa da tsaunin Mandara.

Komawar Buratai yankin arewa maso gabas ya sauya al'amura da yawa - Ndume
Komawar Buratai yankin arewa maso gabas ya sauya al'amura da yawa - Ndume Hoto: Premium Times
Asali: UGC

"Tabbas zuwan shugaban sojojin Najeriya ya kawo banbanci bayyananne. Ya dauki hutu bayan watanni biyu don sake tsarin tunkarar sauran wuraren 'yan ta'addan saboda akwai farar hula da ke yankin.

"Rundunar sojin na neman yadda za ta gujewa yin barnar da za ta shafi jama'a. Suna son tsara yadda za su kawo karshen 'yan ta'addan a karon karshe," Ndume yace.

Ndume ya jajanta tsaikon da ake samu wurin sakarwa sojin kudin aiwatar da manyan ayyuka. Ya kara da cewa dakarun sojin da sauran jami'an tsaron na bukatar goyon baya don sauke dukkan hakkokin da ke kansu.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Ban san abinda ya faru a Abuja ba daga ranar Alhamis, amma ina da tabbacin babu kudin da aka sakarwa sojin na manyan ayyuka tun daga farkon watan shekarar 2020 zuwa yanzu da muke watan Yuni.

"Shugaban kasa na bada umarnin shawo kan matsalar rashin tsaro amma mutanen da ya kamata su sakarwa sojin kudi sun ki yin komai. Wannan abu na tada min hankali," yace.

Ndume ya jinjinawa Gwamna Babagana Zulum a kan kokarinsa na sake gina gidaje don tabbatar da dawowar jama'ar da 'yan ta'addan suka kora.

"Ina son mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Borno a kan kokarinsa da dagewarsa wajen tabbatar da dawowar jama'a yankunan Kirawa, Ashegishar da Ngoshe zuwa gidajensu.

"A halin yanzu, gwamnan na jiran amincewar rundunar soji ne kafin ya bada umarnin dawowar jama'a yankuna da suka bari," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng