Buhari shugaba ne mai hangen nesa - El-Rufa'i

Buhari shugaba ne mai hangen nesa - El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin shugaba mai hangen nesa da ke iya ganin gobe.

A cewar gwamnan, hangen nesa ne yasa shugaba Buhari ya bawa harkar noma fifiko tun bayan hawansa mulkin Najeriya a shekaru biyar da suka gabata.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na rabawa manoma irin noma a jihar Kaduna.

A karkashin shirin raba irin noma ga manoma a fadin Najeriya, ma'aikatar harkokin noma da raya karkara ta kaddamar da rabon irin noma ga manoman jihar Kaduna

Ministan harkokin noma da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono, ne ya kasance jagora yayin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kasance babban bako mai gabatar da jawabi a wurin taron.

"A yanzu haka kasarmu ta hau hanyar cimma wadatuwa a bangaren abincin da muke nomawa a gida kamar su shinkafa, masara da sauransu," a cewar El-Rufa'i.

Gwamnan ya kara da cewa da yanzu 'yan Najeriya sun shiga halin ni 'yasu ba don hangen nesa na shugaba Buhari wajen hana shigo da kayan abinci ba.

Ya bayyana hakan ne yayin alakanta muhimmancin shawarar da Buhari ya yanke a baya da kuma halin da duniya ta shiga sakamakon barkewar annobar korona.

El-Rufa'i ya bukaci 'yan Najeriya su jinjinawa shugaba Buhari saboda irin hangen nesansa, wanda ba dob hakan ba da yanzu kowa ya shiga wahala.

A cewar El-Rufa'i, jihar Kaduna ce a sahun gaban wajen noma kayan abinci irinsu masara, tumatur, gero, wake da sauransu.

Ya ce rabawa manoma iri da basu isashen takin zamani da magunguna kwari da na ciyawa zasu bawa manoma damar rubanya kayan abincin da suke nomawa a baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel