COVID-19: CBN ya rabawa dinbin mutane aron N107.55bn kawo yanzu

COVID-19: CBN ya rabawa dinbin mutane aron N107.55bn kawo yanzu

- CBN ya rabawa mutane da-dama bashin kudi a lokacin annobar COVID-19

- Mutane kimanin 6, 000 ne su ka amfana da bashi na fiye da Naira biliyan 100

- Gwamnati za ta batar da Naira Tiriliyan 1.15 domin ceto tattalin arzikin kasar

Jaridar Daily Trust ta ce akalla Naira biliyan 107.45 aka rabawa mutane a cikin kwanaki 90 da su ka wuce. Alkaluman da su ka fito daga bankin CBN su ka tabbatar da wannan.

Babban bankin na CBN ya bada wannan kudi ne a matsayin aro ga mutane kusan 6, 000. Kamfanoni da kungiyoyi da-dama sun amfana da wannan bashi na gwamnati.

Wannan kudi ya na cikin Naira tiriliyan 1.15 da bankin CBN ya ware domin fitar da jama’a daga cikin kangin da annobar cutar Coronavirus ta jefa Bayin Allah a fadin Najeriya.

Tallafin da bankin CBN ya ke badawa ya hada da Naira biliyan 100 na harkar kiwon lafiya, sai kuma Naira tiriliyan 1 domin bunkasa harkar noma da kuma masana’antun kasar.

KU KARANTA: Yadda Attajirai su ka sha bam-ban da Talakawa wajen halayyarsu

Har ila yau CBN ya ware Naira biliyan 50 a matsayin bashin da za a ba kananan ‘yan kasuwa da sauran jama’a.

Daga cikin kudin kiwon lafiya, an kashe fiye da Naira biliyan 10.

Za a yi amfani da Naira biliyan 100 ne wajen gina wuraren jinya da dakunan kula da marasa lafiya. Daga cikin kudin aikin gona, an batar da Naira biliyan 93.2 kawo yanzu.

Kamfanonin aikin gonan da aka ba wannan kudi sun hada da Greenfield da Brownfield. Mutane kimanin 14, 331 ne su ka amfana da bashin biliyoyin da aka warewa ‘yan kasuwa.

Naira biliyan 4.1 aka rabawa wadannan mutane domin a tada kasuwancinsu da ya ke fuskantar barazana a dalilin annobar cutar COVID-19 da yanzu ta kashe dubunnai a Duniya.

Babban bankin ya sha alwashin fitar da kudi masu yawa domin tallafawa kamfanonin gida. Wannan yunkuri zai taimaka wajen karfafa tattalin Najeriya da samar da ayyukan yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel