Ubangiji ya sanar da ni zan shugabanci jihar Edo - Dan takarar PDP

Ubangiji ya sanar da ni zan shugabanci jihar Edo - Dan takarar PDP

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, Kenneth Imasuagbo ya ce yana da tabbacin cewa zai yi nasara a zabe mai zuwa. Ya yi ikirarin cewa "Ubangiji ya sanar da ni hakan."

Ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi yayin da gidan talabijin din Channels ya karba bakuncinsa a shirin Sunday Politics.

Kamar yadda yace, Ubangiji ya sanar da shi cewa zai zama gwamnan jihar Edo kuma babu wanda ya isa ya hana shi cimma wannan burin.

"Zan zama gwamna, Ubangiji ya sanar da ni haka. Babu wanda mace ta haifa da zai iya hana ni. Zan iya ce muku babu wanda ya isa ya hana ni. Ubangiji da jama'ar jihar Edo na baya na."

Ubangiji ya sanar da ni zan shugabanci jihar Edo - Dan takarar PDP
Ubangiji ya sanar da ni zan shugabanci jihar Edo - Dan takarar PDP Hoto: Channes Television
Asali: UGC

A lokacin da aka tambayesa ko Ubangiji ya sanar masa lokacin da zai shugabanci jihar Edo, ya ce "Lokaci na Ubangiji ne kuma shi kadai ya san lokacin. Amma dole ne nima in nema."

Imasuagbon ya jaddada cewa ba zai daina neman kujerar ba har sai ya samu don yana da jajircewa.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Ba zan daina neman kujerar ba har sai na cimma burina. Ba zan yi kuskure ba don ni mutum ne mai jajircewa," ya yi bayani.

"Duk wanda ya sanni lokacin ina makaranta, ya san ni da jajircewa tare da karfin hali," ya kara da cewa.

Kamar yadda yace, babu dan takara a karkashin jam'iyyar PDP da zai hada kansa da shi a takardun makaranta don haka yana da duk wata cancanta ta shugabantar jihar Edo.

Ya ce ya amfanar da rayukan jama'a da yawa na jihar Edo kuma zai ci gaba da hakan har sai ya zama gwamna.

Hakazalika, matukar an yi zaben fidda gwani yadda ya dace, zai goyi bayan duk wanda ya bayyana a matsayin dan takarar PDP.

"Zan rungumi duk wanda ya yi nasarar samun tikiti kuma zan hada kai wajen yakin neman kujerar da kudina tare da karfina matukar an yi adalci," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng