Yawan karatu, ka gujewa yi don jama’a da bashi, da kuma sauran hanyoyin yin kudi

Yawan karatu, ka gujewa yi don jama’a da bashi, da kuma sauran hanyoyin yin kudi

Jaridar Marketing Mind ta kasar waje ta jero wasu halaye da Attajirai su ka siffanta da su, wanda su ka sa su ka bambanta da marasa hali a duk inda su ke a fadin Duniya.

Ga wadannan halaye ga masu neman bin sahun Attajirai:

1. Ka ƙudiri buri

Ka zama ka na da buri da makusudin da ka ke nufi, ba kurum ka rika tunanin kanzon-kurege ba. Za ka kudiri buri a rayuwa, sannan ka tashi tsaye wajen ganin ka cin ma nufi.

2. Ka da ka biyewa caca

Masu neman nasara a rayuwa ba su tsaya jiran neman sa’a ta hanyar caca. Su na dagewa ne da neman kudi ta hanyar gumi ba da zuwa gidan caca ba.

3. Ka guji gulma

Masu biɗar yin arziƙi sai sun ƙauracewa gulma, su daina yi da wani. Gulmar wani ya na iya jawowa mutum matsala a rayuwa.

4. Ka da ka riƙa saurin cewa ‘A’a’

Ka zama mai lura da abubuwa cikin natsuwa. Ka da ka yi gaggawar cewa a’a ga duk shawarar da aka kawo maka. Bayan ka yi tunani, sai ka ɗauki mataki.

KU KARANATA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

5. Ka dage da karatu

A duk shekara Bill Gates ya na karanta littatafai 50 a Duniya. Wannan ya na taimakawa hamshakin Attajarin wurin buɗa masa ƙwaƙwalwa.

6. Ku rabu da ta mutane

Masu cin nasara a rayuwar Duniya ba su yin abu domin mutane su yaba. Ba su gasar sa tufafi mai tsada ko kuma hawa motocin yayi da rike kayan zamani.

7. Ka zama mai murmushi

62% na Attajirai su kan yi murmushi duk rana, yayin da 16% na marasa hali ne kawai su ke da yawan murmushi. Murmushi zai iya canzawa mutane ra’ayi game da kai.

8. Ka da ka zama mai yawan cin bashi

Attajirai su kan ƙauracewa karɓan aron kudi idan za su saye abu. Su kan adana dukiya ne idan sun yi sha’awar wani abu a maimakon su ci bashi.

9. Ka zama mai kyauta

Gudumuwa, kyauta da tukwuci ga ‘yanuwa da Abokan arziki su zama halinka idan ka na neman dukiya. Ka kuma zama mai bada kyautar lokacinka da koyawa jama’a aiki.

10. Ka haɗa-kai da wasu

Waɗanda su ka karanci nasara rayuwa sun san amfanin haɗa-karfi da karfe da sauran jama’a domin cin ma burinsu. Ka zama mai raba ɗawainiya domin wasu su taso.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel