IPOB ta na batar da $85, 000 duk wata saboda bata Gwamnati – Fadar Shugaban kasa

IPOB ta na batar da $85, 000 duk wata saboda bata Gwamnati – Fadar Shugaban kasa

- Fadar Shugaban kasa ta zargi IPOB da kokarin jawowa Gwamnatin Najeriya bakin-jini

- Mai magana da bakin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kungiyar ta na bata gwamnati

A jiya ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni, 2020, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce kungiyar IPOB ta na yi wa Duniya karyar ana yi wa kiristoci kisan gilla a cikin kasar nan.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya fitar da wani dogon jawabi ya na zargin kungiyar IPOB da yunkurin batawa gwamnati suna.

Garba Shehu ya ke cewa hukumomin gwamnati sun gano cewa kungiyar ta IPOB mai fafutukar neman ‘yancin kasar Biyafara ta na yi wa gwamnatin kasar sharri a waje.

Shehu ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa IPOB da hada-kai da wasu a kasashen waje inda su ke saidawa kasashen waje karyar ana gallazawa kiristocin da ke Najeriya.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

IPOB ta na batar da $85, 000 duk wata saboda bata Gwamnati – Fadar Shugaban kasa
Garba Shehu Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

A Satumban 2017 ne Jami’an tsaro su ka jefa kungiyar IPOB cikin sahun ‘yan ta’adda a Najeriya, kuma aka gargadi iyaye da su daina barin ‘ya ‘yansu su shiga wannan kungiya.

A yanzu an gano wannan kungiya ta ‘yan ta’adda su na amfani da rigar addinin wajen kira ga jami’an Amurka su kawo karshen muzgunuwar da ake yi wa kiristoci a kasar.

Hadimin shugaban na Najeriya ya ce burin wannan mugun aiki shi ne a jawo gaba tsakanin gwamnatin Najeriya da manyan kasashen Turai da kuma kasar Amurka.

Fadar shugaban kasar ta ce tun Oktoban 2019 IPOB ta ke kashe $85, 000 domin cin ma wannan buri, har zuwa yanzu babu wanda ya san inda ake samun wadannan kudi.

“Ana ba Najeriya da kasashen ketare shawarar su bi a hankali da wannan yunkuri da ake yi na batar da jama’a, wanda hujjoji su ka nuna duk wata ana kashewa $85, 000.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel