An damke mai cutar Korona da ta gudu a daga jihar Imo a jihar Ondo tana sayar da gwanjo

An damke mai cutar Korona da ta gudu a daga jihar Imo a jihar Ondo tana sayar da gwanjo

Kwamitin yaki da cutar Coronavirus na gwamnatin jihar Ondo ta damke wata mata mai cutar da ta gudu daga jihar Imo a kasuwar Oja Oba dake babbar birnin jihar, Akure, tana sayar da gwanjo.

An damke wannan matar ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni, 2020, rahoton Punch.

Kwamishanan lafiyan jihar Ondo, Dakta Wahab Adegbenro, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Akure inda yace matar ta gudo jihar ne daga Imo duk da dokar hana sufuri tsakanin jihohi.

A cewar kwamishanan, matar mai dauke da cutar "ta kamu da cutar ne a can jihar imo amma ta gudo jihar Ondo ba tare zuwa asibiti ba."

Ya yi bayanin cewa bayan guduwanta, gwamnatocin Imo da Ondo sun bazama nemanta.

Yace: "Daga baya aka damketa a inda take sayar da kayan gwanjo a kasuwar dake Akure."

Adegbenro ya kara da cewa an fara bibiyan wadanda sukayi mu'amala da ita cikin yan'uwa, abokar, da makwabta.

Ya yi kira ga dukkan wadanda sukayi harkallar kasuwanci da ita su gabatar da kansu domin gwaji.

Adegbenro ya yi kira ga al'ummar jihar Ondo suyi zamansu a gidan sai idan suna da wani abu muhimmi da suka bukaci yi a waje, saboda cutarta fara yaduwa tsakanin unguwanni yanzu.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Abiya, Okeazie Ikpeazu, ya kamu da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, ta ce, ta turawa yan Najeriya sakonnin wayar da kai kan cutar Coronavirus sama da milyan dari (100m) daga watan Febrairu zuwa yanzu.

Hukumar wacce ta bayyana hakan ranar Asabar a shafinta na Tuwita, ta alanta kwanaki 100 da bullar cutar Korona a Najeriya da ta hallaka akalla mutane 300.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel