Ba na damuwa da yadda Jama’a su ke yi wa Ingilishina dariya – inji Hon. Gudaji Kazaure

Ba na damuwa da yadda Jama’a su ke yi wa Ingilishina dariya – inji Hon. Gudaji Kazaure

- Muhammad Gudaji Kazaure ya ce bai damuwa da yadda a kan yi masa dariya

- Ana kukan cewa Dan Majalisar Tarayyar bai kware sosai a harkar Turanci ba

- Kazaure ya ce abin da ake bukata shi ne yare ya rika isar da sakon da aka nufa

Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana dalilin da ya sa ba zai rika amfani da harshen Hausa wajen magana a gaban majalisa, ganin yadda wasu su kan yi masa dariya ba.

‘Dan majalisar ya yi hira da jaridar BBC Hausa ta shafin Instagram inda ya ce ya kan yi amfani da Ingilishin ne domin idan ya yi magana ko Bature ne ya ji, zai iya gane inda ya dosa.

Gudaji Kazaure ya ce hakazalika shi ma idan Bature ya yi masa Ingilishi, zai gane duk abin da ya ke nufi, don haka ya ce babu dalilin da zai ki magana da wannan yare da ya iya sa.

Kazaure ya ce dama ainihinsa kasuwanci ya sa gaba: “Ni ba ‘Dan Boko ba ne, asalina da na taso, ‘dan kasuwa ne. Na yi karatu na daidai gwargwado, daga nan na tafi neman kudi.

“Ni abin da na yarda da shi, shi ne yare akwai na ka, akwai wanda ba na ka ba. Turanci aro sa mu ka yi, domin Turawa ne su ka yi mana mulkin mallaka, su ka kawo mana Boko.”

KU KARANTA: Albashi na ba ya wuce mako guda ya kare sai in koma kame-kame- Kazaure

“Idan dai za ka fadi gundarin sako ya je wa al’umma yadda za su gane shi ke nan. Babu wanda ke jin Turanci wanda zan yi magana, ya ce bai fahimta ba. Shiyasa na ke Ingilishi.”

‘Dan siyasar ya ke cewa ko Talaka zai iya gane Ingilishin da ya ke yi a zauren majalisa. “Domin ni mafi yawan mutanena manoma ne, Turanci na ke yi masu kamar Hausa, su fahimta.”

Ya kuma ce: “Babu ruwana da wasu ka’idojin Turanci, dama ni ba Bature ba ne. Idan zan yi magana a gane, duk wanda zai ce ban iya ba, ya yi ta fada, ko damuwa ba na yi.”

‘Dan majalisar na Kazaure, Gwiwa, Roni da ‘Yankwashi ya ce ya je kasar Ingila ya iske Jakadan Faransa da tafinta, inda ake fassara masa harshen na Ingilishi zuwa yarensa na Faransa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel