Kwadayin kujerar gwamna: Mataimakin gwamnan APC ya kammala shirin komawa PDP

Kwadayin kujerar gwamna: Mataimakin gwamnan APC ya kammala shirin komawa PDP

Jaridar The Nation ta rawaito cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Honarabul Ajayi Agboola, zai iya sanar da komawarsa jam'iyyar PDP a cikin sati mai zuwa.

The Nation ta ce majiyarta ta sanar da ita cewa Honarabul Agboola zai koma jam'iyyar PDP ne domin yin takarar kujerar gwamna da ubangindansa, gwamna mai ci, Rotimi Akeredolu, wanda aka zabesu tare a karkashin inuwar jam'iyyar APC a shekarar 2016.

Tuni dangantaka tsakanin Honarabul Agboola da gwamna Akeredolu ta lalace bisa matsalolin zargin rashin yarda da cin amana.

Majiyar jaridar ta sanar da ita cewa wasu daga cikin mambobin jam'iyyar APC a majalisar dokokin jihar Ondo za su koma jam'iyyar PDP tare da mataimakin gwamnan.

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ondo a PDP a shekarar 2016, Eyitayo Jegede, ne ya fara nuna cewa Honarabul Agboola zai koma jam'iyyar PDP.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya sayi fom dinsa nasake tsayawa takarar neman kujerar gwamnan jihar Ondo a zaben da za a yi a watan Oktoba na shekarar nan.

Jegede ya bayyana cewa dawowar Honarabul Agboola zuwa PDP "ya nuna cewa gidan jam'iyyar APC ya rushe, a saboda haka dole Agbooola ya nemi gida mai kyau".

A cewar Jegede; "da APC jam'iyyar kirki ce, Agboola ba zai barta ba. Da PDP jam'iyyar banza ce, ba zai zabi ya dawo cikinta ba.

Kwadayin kujerar gwamna: Mataimakin gwamnan APC ya kammala shirin komawa PDP
Ajayi Agboola
Asali: UGC

"Kundin tarihin jam'iyya ya gayyama fayyace komai. Zai je mazabarsa ya yanki rijista. Zai je gaban kwamitin gudanarwa ya nemi izinin yin takara bayan dawowarsa.

"Bayan ya kammala duk wannan, zai zo ya biya sauran kudaden da jam'iyya ke cajar manyan sabbin mambobi. Daga nan kuma zai iya sayen fom din takara.

DUBA WANNAN: NAHCON ta yi karin haske a kan yiwuwar yadda za a gudanar da aikin Hajjin bana

A ranar Laraba ne Legit.ng ta rawaito cewa wani kwamitin sulhu da jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ta kafa ya sanar da cewa tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, ya koma tsohuwar jam'iyyarsa bayan ya shafe tsawon shekaru 6 a jam'iyyar APC.

Kwamitin ya bayyana cewa ya yi matukar farin cikin samun nasarar shawo kan Oni har ya amince ya dawo jam'iyyar PDP tare da 'yan gani kashenin magoya bayansa.

A cewar kwamitin, dawowar Oni ba kankanuwar nasara ba ce ga mambobin kwamitin da shugabanci jam'iyyar PDP na jihar Ekiti.

Kazalika, kwamitin ya yi kira ga tsohon ministan aiyuka, Sanata Adedayo Adeyeye, da sauran wadanda su ka bar PDP da su dawo jam'iyyar.

Adeyeye ya fice daga jam'iyyar PDP ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2018 bayan ya sha kasa a hannun Farfesa Kolapo Olusola a zaben fidda dan takarar jam'iyyar PDP.

Bayan fitarsa daga PDP, Adedeye ya koma jam'iyyar APC inda ya hada kai da dan takararsu, Dakta Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti mai ci.

Da su ke ganawa da manema labarai ranar Litinin a Ado-Ekiti, shugaban kwamitin, Sanata Hosea Agboola, da sakatarensa, Diran Odeyemi, sun gargadi sauran mambobin jam'iyyar PDP a kan nuna wata halayya da kan iya kawo nakasu a kokarin sulhun da ake yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel