Ke duniya: Budurwa tare da hadin bakin saurayinta ta yi garkuwa da kanta

Ke duniya: Budurwa tare da hadin bakin saurayinta ta yi garkuwa da kanta

- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wata budurwa mai shekaru 17 tare da saurayinta sakamakon zarginsu da ake yi

- Mahaifiyar ta kai wa 'yan sandan rahoton cewa an yi garkuwa da diyarta tare da bukatar naira dubu dari biyar a matsayin kudin fansa

- Bayan bazamar 'yan sanda, an samo budurwar tare da saurayinta a wata maboya inda ya tabbatar da cewa hada baki suka yi

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wata budurwa mai shekaru 17 mai suna Seun Adekunle tare da saurayinta mai suna Basit Olasunkanmi.

An kama su ne sakamakon zarginsu da ake da hadin baki wajen garkuwa da budurwar.

Wannan na kunshe a wata takarda da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya bai wa manema labarai a Abeokuta.

Oyeyemi ya ce, "An kama su biyun bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar mai suna Bukky Adekunle ta kai wa 'yan sandan Enugada har ofishinsu.

"Ta kai rahoton ne a ranar Alhamis a kan cewa ta aika budurwar kasuwa da ke Abeokuta a ranar 1 ga watan Yunin 2020 amma bata dawo ba."

Ke duniya: Budurwa tare da hadin bakin saurayinta ta yi garkuwa da kanta
Ke duniya: Budurwa tare da hadin bakin saurayinta ta yi garkuwa da kanta. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ta kara da cewa "Ta samu kiran wani bayan kwanaki biyu inda aka yi ikirarin cewa an yi garkuwa da ita kuma ana bukatar kudin fansa har naira dubu dari biyar idan tana son ganin diyarta a raye."

Mahaifiyar ta ce, "Mai kiran ya kara da jan kunnenta da kada ta kuskura ta kai rahoto wurin 'yan sanda matukar tana fatan ganin diyarta a raye."

Ya kara da cewa, DPO din Enugada, SP Baba Hamzat ya jagoranci rundunar jami'an tsaro idan suka gano budurwar da saurayinta a wata maboya.

Tuni aka damke su tare da kawo su ofishin 'yan sanda.

Oyeyemi ya ce binciken farko ya bayyana cewa saurayin wanda mahauci ne, ya hure wa budurwar kunne inda ya ja ta zuwa aiwatar da muguwar manufarsa saboda yana matukar bukatar kudi.

Amma kuma, kwamishinan 'yan sandan jihar CP Kenneth Ebrimson ya bada umarnin gaggauta mika al'amarin hannun sashen binciken manyan laifuka don ci gaba da bincike tare da gurfanarwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164